Gobarar tankar mai ta kashe da mutane a Jos

0
85

Wani kazamin hadarin motar daukar mai a birnin Jos da ke Jihar Filato ya yi sanadiyar rasa rayuka da kuma asarar dukiyoyi masu yawa.

RFI ya ruwaito cewa tankar mai ce ta kwace inda ta afkawa wasu ababen hawa kana ta kama da wuta, abin da ya yi sanadiyar samun gobarar.

Zakari ya ce motoci da dama sun kone, tare da rasa rayuka, yayin da aka fuskanci matsala wajen kashe gobarar saboda rashin isar motocin ’yan kwana-kwana da wuri.

Bidiyon da shaidun gani da ido suka dauka sun nuna yadda wasu jama’a ke dibar ruwa da kuma kasa suna kokarin kashe wutar.

Wakilinnmu wanda ya tattauna da wata mata da ta bayyana masa bacewar yaranta biyu da kuma jami’in agaji na Red Cross da shaidun gani da ido, ya ce ya ga gawarwakin mutane 8 da gobarar ta ritsa da su.

An dai samu hadarin ne akan mararrabar hanyar da ta fito daga Jami’ar Jos inda ake da mahadar hanyoyin da suka tafi Bauchi da Zaria da kuma cikin garin Jos.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here