Najeriya, Ghana na kwashe ‘ya’yansu daga Sudan

0
107

Ghana ta kwashe ‘ya’yanta 82 daga Khartoum, babban birnin Sudan yayin da kasashe ke ta kokarin kwaso jama’arsu daga kasar sakamakon yakin da ake gwabzawa tsakanin rundunar soji da dakarun Rapid Response Forces, RSF.

Kamfanin dillancin labarai na Ghana ne ya sanar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ma’aikatar harkokin wajen Ghana da hadin gwiwar ofisoshin jakadancin kasar da ke Alkahira da Addis Ababa da Khartoum ne suka yi wannan aikin.

Ta ce tun da farko mutum 50 ne aka soma kwasowa sa’annan aka kwaso mutum 27 inda aka ajiye su a Gedaref da ke kan iyakar Sudan da Habasha. Wadanda aka kwason sun hada da mata 34 da maza 43.

Bugu da kari akwai ‘yan kwallon kafa na Ghana uku da wasu mutum biyu da ke aiki a kamfanin hako ma’adanai na kasar Australiya da aka ceto.

Hakan ya sa jumullar wadanda aka kwaso zuw yanzu ya kai mutum 82.

Ma’aikatar harkokin wajen ta Ghana ta bayyana cewa a yau za a wuce da su garin Metema da ke cikin Habasha wanda shi ma yake kan iyaka inda za a karbe su domin yi musu bizar shiga Habasha. Daga nan ne za a wuce da su kasar Ghana.

Wane hali ‘yan Nijeriya da ke Sudan ke ciki?

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa ko runtsawa ba ta yi domin ganin an kwashe ‘yan kasar daga birnin Khartoum da ake yaki.

Ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya da hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar da hukumar da ke kula da ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje ne ke aikin kwaso ‘yan kasar daga Sudan.

A bayanai na baya-baya da aka samu sun nuna cewa gwamnatin Nijeriya ta biya wani kamfanin sufurin motoci naira miliyan 150 domin kwaso ‘yan kasar.

Gwamnatin Nijeriya ma ta wallafa hotunan dalibai suna bin layin shiga motocin da za su kwashe su zuwa Masar.

Shugabar hukumar kula da ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje Abike Dabiri ce ta wallafa a shafinta na Twitter inda ta ce daga nan za a kwashe su a jiragen sama zuwa Nijeriya.

Tuni dama kamfanin jirgin sama na Air peace na Nijeriya ya ce a shirye yake domin ya taimaka wurin kwaso ‘yan Nijeriya da suka makale a Sudan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here