Yakin Sudan: ’Yan Najeriya miliyan 3 ne ke neman guduwa daga Sudan – Abike

0
264

Shugabar hukumar kula da ’yan Najeriya mazauna ketare, Abike Dabiri-Erewa, ta ce akwai ’yan asalin Najeriya akalla miliyan uku a kasar Sudan inda yaki ya rincabe, kuma gwamnati tana fadi-tashin kwaso duk ’yan Najeriya da yakin ya rutsa da su zuwa gida.

Abike ta bayyana cewa a safiyar Talata ake sa ran fara kwaso ’yan Najeriyan da yakin ya ritsa da su, bayan samun sahalewar bangarorin sojin da ke yakar juna a Sudan.

Daga cikin ’yan Najeriya mazauna Sudan akwai dalibai kimanin 5,000 wadanda suka bayyana matukar kaduwa bayan barkewar yakin, wanda ya haddasa rashin ruwan sha da abinci da kudi da layin sadarwa a Khartoum, babban birnin kasar.

A baya-bayan nan rikici ya kara rincabewa a Sudan tsakanin bangaren gwamnatin rikon kwaryar kasar da mayakan RSF kan shugabanci.

A ranar Karamar Sallah bangarorin biyu suka amince da tsagaita wuta na kwana uku domin bukukuwan sallar, amma ba a jima ba a ranar aka ci gaba da luguden wuta a Khartoum.

Rikicin da ya yi ajalin daruruwan mutane gami da jikkata wasu ya kai ga rufe filayen jirgin sama kasar, inda daliban Najeriya kimanin 5,000 ne suke karatu.

A kan haka ne aka yi tsarin da daliban za su tsallaka zuwa Habasha, inda daga nan za a kwaso su zuwa gida, ta hannun Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya.

Aminiya ta ruwaito a ranar Lahadi cewa kamfanin jiragen sama na Air Peace ya yi wa gwamnati tayin kwaso su kyauta zuwa gida.

Shugaban Air Peace, llen Onyema, ya ce idan ’yan Najeriyan da ke Sudan suka tsallaka zuwa kasashen makwabtakan Sudan, to kamfaninsa zai kwaso su zuwa gida a kyauta.

Ya ce aikin kwaso su ya wuce a bar wa gwamnati ita kadai, saboda bai kamata a yi asarar dan Najeriya ko daya ba a rikicin na Sudan.

Hakan kuwa na zuwa ne bayan Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin ranar Talata za ta fara kwaso ’yan Najeriyan ta kasar Habasha.

Wannan kuwa, wani sabon mataki ne, bayan da farko gwamnatin ta ce kwaso daliban kai-tsaye daga Sudan abu ne mai matukar wuya kasancewar an rufe sararin samaniyar kasar.

A ranar Asabar, wata sanarwar kungiyar daliban Najeriya da ke Sudan ta ayyana wasu wurare uku da daliban za su hadu a Sudan domin a kwashe su zuwa Habasha.

Tun da farko, wasu daga cikin daliban sun bayyana cewa komai na iya faruwa da su saboda yadda bangarorin sojin da ke yakar juna suke luguden wuta babu kakkautawa a Khartoum.

Wasu daga cikinsu sun bayyana cewa kasashe, hatta wadanda ke fama da yaki, irin su Syria, da irin su Malawi wadda ba ta da ofishin jakadanci a Sudan, sun riga sun kwashe dalibansu zuwa gida.

Sun kuma bayyana damuwarsu cewa katse layin sadarwa da rikicin ya haddasa na iya kawo tasgaro ga yadda za a tuntube su domin kwashe su daga kasar ba tare da an bar wasu a baya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here