Sojoji sun kashe ‘yan ta’addan Boko Haram 35, sun tarwatsa sansanoni 12 a dajin Sambisa

0
136

Dakarun rundunar soji ta bataliya ta 21 da ke Bama da bataliya ta musamman ta 199 da kuma ‘yan sakai sun kashe ‘yan ta’addan Boko Haram 35 a wani samame da suke kai a dajin Sambisa.

Sojojin karkashin jagorancin Birgediya Janar Victor Unachukwu (Emperor), sun kai farmakin ne na musamman a maboyar ‘yan Boko Haram din a kokarin da rundunar ke yi na ganin ta kakkabe burbushin duk ragowar ‘yan ta’addan da ke dajin Sambisa.

A cewar rahoton leken sirri da Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da tada kayar baya kuma manazarci kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, ya nuna cewa, rundunar ta fara kai farmakin kakkabe ragowar ‘yan ta’addan ne daga garin Awulari a ranar 17 ga watan Afrilu.

A karshen wannan farmakin na musamman na kwanaki uku, sojojin sun yi nasarar kawar da maboyar ‘yan ta’adda a garuruwan Garno, Alafa, Alafa D, Garin Dakta, Njumia, Izzah, Farisu, Somalia, Ukuba, Garin Glukose, Garin Ba’aba da Bula Abu Amir dukkansu a karamar hukumar Bama a jihar Borno.

A cikin wannan samame an kubutar da wasu mata da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here