Rikicin Sudan ya lafa bayan Janar-Janar sun amince su tsagaita wuta

0
107

Da alamu fafatawar da ake yi tsakanin rundunar sojin Sudan da dakarun rundunar Rapid Response Forces (RSF) da ba na gwamnati ba ta dan lafa a wasu bangarori na Khartoum, babban birnin kasar bayan an yi ta kira a gare su da su tsagaita wuta don yin shagulgulan Sallah.

Fiye da mutum 400 ne suka mutu yayin da dubbai suka jikkata tun bayan da fada ya kaure ranar Asabar tsakanin rundunar soji karkashin jagorancin babban hafsan soji Abdel Fattah da mataimakinsa, Mohamed Hamdan Daglo da aka fi sani Hemeti, wanda ke shugabantar rundunar (RSF).

Ranar Juma’a rundunar sojin ta sanar cewa ta “amince ta tsagaita wuta ta kwana uku” domin “bai wa ‘yan kasar damar yin bikin karamar Sallah da kuma bari a kai kayan agaji”, kamar yadda Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da Sakataren Wajen Amurka Antony Blinken suka bukaci a yi.

Ganau a yankuna da dama na Khartoum sun ce an kwashe tsawon Juma’a ba tare da jin karar harbe-harbe da luguden wuta ba.

Karamar sallah lokaci ne da ya kamata “a raba alawa da cincin, ga kuma yara cikin farin ciki sannan mutane su je gaisuwar sallah”, in ji wani mazaunin Khartoum Sami al-Nour a hira da kamfanin dillancin labarai na AFP.

Sai dai maimakon hakan, ya ce sun yi ta jin “luguden wuta da kuma warin jini a unguwanninmu”.

Sojoji da mayakan RSF sun yi zafafan arangama a yankunan da ke da jama’a sosai na Khartoum, inda shaidu suka bayar da rahoton jin karar fashe-fashe kusa da hedikwatar rundunar soji a birnin da ke da mutum miliyan biyar.

Tun da farko rundunar RSF ta amince ta tsagaita wuta ta awa 72.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce an kashe mutum 413 yayin da aka jikkata fiye da 3,551 a fadan da ya kaure a fadin Sudan, sai dai rahotanni sun ce adadin ya zarta haka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here