Rikicin Sudan: An fara kwashe ‘yan Saudiyya daga Sudan

0
99

Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta fara kwashe ‘yan ƙasar da kuma wasu ‘yan ƙasashen Larabawa da ma sauran jama’ar ƙasashe abokan ƙawance.

Rundunar sojojin Sudan ta faɗa a yau Asabar cewa, an fara tsare-tsaren kwashe jami’an diflomasiyya da mutanen ƙasashen Larabawa da ke son fita daga Sudan.

Matakin na zuwa ne bayan tattaunawa da Shugaban Majalisar Iko da Iyakokin ƙasar, Laftanal Janar Abdel Fattah Al-Burhan, da shugabannin wasu ƙasashe game da hanyar da za a tabbatar da kwashe mutanen.

An kwashe jami’an ofishin jakadancin diflomasiyyar Saudiyya ta ƙasa zuwa yankin Port Sudan daga nan kuma aka kwashe su a jirgin sama zuwa Masarautar Saudiyya.

Haka kuma an tsara cewa su ma jami’an diflomasiyyar Jordan za a kwashe su ne ta irin wannan hanya.

Yayin da ƙazamin yaƙin Sudan yake shiga makonsa na biyu, ƙasashe da yawa sun yanke shawarar kwashe mutanensu daga Sudan, kuma su ci gajiyar yarjejeniyar tsagaita wuta mai tangal-tangal don kwashe ‘yan ƙasashen waje.

Dakarun RSF sun nuna muradinsu na taimaka wajen sake buɗe filayen jiragen sama don sauƙaƙa aikin kwashe ‘yan ƙasashen wajen.

Majalisar Ɗinkin Duniya da Amurka da Burtaniya da Japan da Switzerland da Koriya ta Kud da Sweden da Sifaniya na tattaunawa kan shirye-shiryen kwashe ma’aikatansu daga Khartoum.

Sojojin Jamus sun fara shirye-shirye a wani sabon yunƙuri na kwashe ‘yan ƙasarsu daga Sudan, bayan sun gaza yin haka a yunƙurin da aka yi a baya saboda al’amari ya ƙazance.

Ƙasashen Yamma da China za su kwashe jami’an diflomasiyyansu da kuma mutanensu da jiragen sojoji na dakon kaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here