DSS ta kama ‘yan bindiga a Kano

0
147

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya a Nijeriya DSS ta ce ta kama wasu ‘yan bindiga biyu dauke da makamai a Jihar Kano da ke arewacin kasar.

Wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na intanet ranar Alhamis, ta ce ta kama mutanen ne yayin da suke kan hanyarsu ta kai makaman wata jiha da zummar kaddamar da hare-hare.

Sanarwar, wadda kakakin DSS, Peter Afunanya ya sanya wa hannu ta kara da cewa an kwace makamai daban-daban daga hannun ‘yan bindigar.

Abubuwan da aka kama sun hada da bindiga kirar AK-47 guda biyu da kwanson harsasai na AK47 shi ma guda biyu da babur guda daya da kuma wani buhun doya da aka boye bindigogi.

“Hakan ya nuna cewa akwai bukatar mutane su lura da kyau sannan su kai rahoto ga jami’an tsaro da ke kusa da su kan duk wani motsi na mutanen da ba su amince da su ba,” in ji Afunanya.

Hukumar tsaro ta yi kira ga wuraren shakatawa da su sanya ido sosai a lokacin bukukuwan karamar Sallah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here