Buhari ya nemi ‘yan Najeriya su yi masa afuwa

0
116

Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi afuwar ‘yan Najeriya game da mulkin da ya yi tsawon wa’adi biyu daga 2015 – 2023.

Ya dai nemi duk wanda ya ɓatawa, ya yafe masa.

Yayin jawabinsa na ƙarshe ranar Juma’a a bikin Sallar Idi wanda daga ita zai miƙa mulki, Buhari ya gode wa ‘yan Najeriya saboda amincewar da suka yi da shi ya ja ragamar ƙasar tsawon shekara takwas.

Wata sanarwa da Mallam Garba Shehu, mataimakin shugaban ƙasar na musamman kan harkar yaɗa labarai ya fitar, ta bayyana irin gudunmawar da Buhari ya bayar ta fuskanci shugabanci cikin sama da shekara 40.

Ya riƙe muƙamai masu yawa a matsayin jami’in soja, ya yi gwamnan jiha a lokacin mulkin soja. Ya kuma yi minista a Najeriya kafin ya zama shugaban ƙasa na mulki.

Kuma daga bisani ya sake dawowa shugabancin Najeriya a matsayin jagoran farar hula a 2015.

Daidai lokacin da ya rage ƙasa da kwana 37 ya sauka daga mulki, Shugaba Buhari ya ce tafiyar ta cike take da ƙalubale ciki har da ɗaurin da aka yi masa a gidan yari tsawon shekara uku bayan hamɓarar da shi daga kan mulki a watan Agustan 1984.

Haka kuma, sau uku yana faɗuwa zaɓe, lokacin da yake takarar shugaban ƙasa a 2003 da 2007 da kuma 2011.

“Na shigar harkar ‘yan siyasa, ƙarshe dai har sau uku ina danganawa da Kotun Ƙoli.

Sun yi ta mini dariya, ni kuma na ce “Ai Allah yana nan”.

Ubangiji ya kawo min ɗauki ta hanyar ci gaban fasaha, ta hanyar kantin zaɓe na dindindin PVC.

Shugaba Buhari ya ce maganar amfani da ƙabilanci ko addini a harkar zaɓe ‘shashanci ne kawai’ don kuwa alƙalan Kotun Ƙolin da suka yi watsi da ƙararrakinsa, Musulmai ne daga Arewa, ɗaya ya fito daga Zaria a jihar Kaduna akwai ɗan jihar Neja da kuma na Jigawa.

“Yana da kyau kuma na yi bayani a kan abubuwan da aka saba yi a nan. A Abuja, musamman kan al’amuran tsaro.

Tsaro ba kawai magana ake yi a kan Arewa maso Gabas ba, rashin tsaron ya fantsama zuwa Abuja da sauran wurare a Najeriya.

“Mun murƙushe waɗanda suka ƙaraso nan Abuja da zimmar hana rayuwa ɗadi, mun yi maganinsu,” ya ƙara da cewa.

Shugaba Buhari ya nuna muhimmancin dimokraɗiyya, da yadda take samar da dama ga jama’a su shiga a dama da su cikin harkokin mulki, da kuma sanya wa mutane jin cewa ƙasarsu, tasu ce.

“Ina ƙirga yadda shekaru suke tafiya.

Dimokraɗiyya na da kyau, idan ba haka ba, yaya za a ce mutum daga wani saƙon Najeriya ya zo ya shugabanci ƙasar tsawon shekara takwas?”

“Garin da aka haife ni, ba shi da nisa bai fi kilomita takwas ba tsakaninsa da Jamhuriyar Nijar.

“Idan ministan man fetur ya nemi ya rufe gidajen mai da ke da nisan kilomita 10 da Daura, muna da gidajen mai kusa da mu”, a cewarsa.

Shugaban ya ce ya yanke shawarar koma wa Daura, wadda ta yi nesa da Abuja don ya huta, bayan ya shafe gomman shekaru yana aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here