Mutum miliyan 2.5 ne suka halarci saukar Al’qur’ani a daren 29 a masallacin Makkah

0
114

Sama da masu ibada miliyan 2.5 ne suka halarci saukar Al-Qur’ani a daren 29 na watan azumi, a babban Masallacin Juma’a na Makkah. Cikin mutanen har da masu aikin Umarah da kuma waɗanda sallar ce kawai ta kai su.

Sheikh Abdurahman Al-Sudais, babban limamin Masallacin Harami guda biyu ne ya jagoranci sallar a babban Masallacin Juma’a, wanda mutane sama da miliyan biyu suka halarta.

Masallacin Harami guda biyu sun cika makil da masu ibada har ma da titunan da ke kewaye da su.

Da yake jagorantar addu’o’in, Sheikh Al-Sudais ya roki Allah Maɗaukakin Sarki da ya gafarta wa dukkan musulmi a wannan dare mai albarka, ya kuma tseratar da su daga shiga wutar jahannama.

Ya kuma yi addu’ar Allah ya ci gaba da kare Masarautar Saudiyya da shugabanninta da kuma dukkan ƙasashen musulmi daga dukkan sharri, ya kuma ba su lafiya da kwanciyar hankali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here