Wata mata ta maka mijinta a kotun Musulunci kan rashin kaita Saudiyya

0
138

Wata matar aure, Karima Nuhu ‘yar shekara 45, ta maka mijinta Musa Falalu a kotun shari’ar Musulunci da ke a gundudumar Rigasa a karamar hukumar Igabi a Jihar Kaduna kan zarginsa da kin kaita Saudiyya.

Karima wadda ta ke da zaune a Rigasa, ta shaida wa kotun cewa, shekarunta hudu da auren Falalu, amma a wata biyu kacal ya ciyar da ita abinci.

Ta shaida wa kotun hakan a ranar Talata, inda ta ce, Falalu ya shaida mata cewa ya rasa aikinsa na tukin mota, amma ya samu wani aikin a Saudiyya, inda ya roke ta kara yin hakuri, zai tafi da ita zuwa Saudiyya.

A cewarta, a yanzu ni nake ciyar dabshi kuma ina karbo masa bashin kudi don ya biya mana kudin da zamu tafi zuwa Saudiyya, bayan ya samu abinnda yake bukata, ya sake ni.

Ta shaida wa kotun cewa, ita ba ta da wata shaida sai Allah kuma shi ne zai yi hukuunci a tsaninta da shi a gobe kiyama.

Sai dai Falalu ya karyata zagin da ta ke yi masa, domin ya riga ya sake ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here