Kotu ta tsare mutum biyu kan kashe abokin su akan Naira dubu 65,000 a Kwara

0
189

Wata Kotun Majistare da ke Ilorin a Jihar Kwara ta tasa keyar Olasunkanmi Olarewaju (Abore) da Adeniyi Juwon (Jboy) bisa zargin kashe wani Abiodun Oyinloye har lahira.

An gurfanar da wadanda ake zargin ne a gaban kotun bisa tuhume-tuhume biyu da suka hada da hadin baki da kuma kisan kai wanda ya sabawa sashi na 97 da 221 na kundin shari’ar masu aikata manyan laifuka.

A cewar rahoton farko na ‘yan sanda “A ranar 9 ga watan Afrilun 2023 da misalin karfe 7:00 na safe, wani Olasunkanmi Olarewaju (Abore) ya kira waya cewa shi da kansa Olasunkami Olarewaju (Abore) da Adeniyi Juwon (Jboy) sun kashe Abiodun Oyinloye bisa zarginsa da laifin sace masa Naira N65,000

“Nan da nan, jami’an ‘yan sanda sukai gaggawar cafke Olasunkami Olarewaju (Abore) da Adeniyi Juwon (Jboy), dukkansu a wurare mabanbanta a garin Omu-aran.

A hukuncin da ya yanke, Alkalin Kotun Mai shari’a M. O. Abayomi, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare su tare da dage shari’ar zuwa ranar 11 ga Mayu, 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here