Home Labarai Labaran Duniya An sanya dokar hana fita a wasu kauyukan India bisa hare-haren damisa

An sanya dokar hana fita a wasu kauyukan India bisa hare-haren damisa

0
141

Hukumomi a Arewacin India sun sanya dokar hana fita a wasu kauyukan yankin daga karfe 7 na yammaci zuwa 6 na safiya, sakamakon dirar mikiya da wasu damusoshi ke yi akan jama’a bisa abinda aka baiyana cewa karin adadin su da aka samu a yankunan ne ke haddasa wannan iftila’in.

An sanya dokar ne a gundumomi biyu a jihar Uttarakhand, sannan an rufe makaratu na tsawon kwanaki biyu daga ranar Litinin a matsayin kariya ga yankin.

A makon jiya gwamnatin India ta ce adadin damusoshin a kasar ya haura sama da 3,000 da aka sani a baya.

Mahukunta sun baiyana cewa, sun fara samun rahoton farmakin dabbobin ne tun a ranar alhamís da ta gabata  sannan na biyun kuma a ranar Lahadi ba tare da faiyace kisan ko na dabbobin bane a wancan lokacin, abinda ya sanya daukar matakin cikin gaggawa.

Hukumomin sun bayyana cewa, rashin muhalli da damusoshin ke fuskanta sakamakon fadada birane ke sanya su kwararowa cikin jama’a.

A shekarar da ta gabata ne dai wani Dan sanda ya harbe wata damusa da ta kashe akalla mutane 9 a gabashin kasar ta India.

Dama dai kasar India da ke kudancin Asia ne ke dauke da kaso 75 na adadin damusoshin dake duniya, bisa kidayar su da aka gudanar a fadin duniya a makon daya gabata, wanda ya nuna kasar ce keda akalla damusoshi 3,167.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here