Ba mu yarda da sakamakon zaɓen Kano da aka kammala ba – NNPP

0
108

Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta ce ba ta gamsu da zabukan ƴan majalisu da aka karasa ba a ranar Asabar 15 ga watan Afurilu.

Jam’iyyar ta ce ba ta yarda da sakamakon ba ne kasancewar tana zargin cewa an tafka magudi a wasu wuraren da aka yi zaben.

Jihar Kano ce ke da ƴan majalisu mafi yawa na jiha wadanda zaɓen su bai kammala ba a zaben 18 ga watan Maris 2023, inda aka kammala zaben a ranar Asabar 15 ga watan Afrilu, kuma aka an sanar da sakamako.

A sakamakon da INEC ta bayyana, jam’iyyar APC ta lashe mazabar dan majalisar wakilai na Tudun Wada da Doguwa, yayin da NNPP kuma ta samu nasara a karamar hukumar Fagge.

Sai zaben ‘yan majalisun dokokin jiha goma sha hudu inda jam’iyyar APC ta samu goma da Gezawa da Tudun Wada da Gwarzo da Makoda da Dambatta da Warawa da Gaya da Dawakin Tofa da kuma Takai da Wudil.

NNPP ta samu kujeru hudu, wadanda suka hada da Ugogo da Gabasawa da Ajingi da kuma Garko.

Sai dai jam’iyyar NNPP, wadda ita ce ta lashe zaben gwamnan jihar ta nuna rashin gamsuwa da yadda zaben ya gudana.

Umar Haruna Doguwa wanda shi ne shugaban jam’iyyar a jihar Kano, ya ce “Akwai abubuwa da dama da suka faru waɗanda ba mu gamsu da su ba, waɗanda kamar an mayar da hannun agogo baya ne.”

Ya yi zargin cewa an tayar da hankula a wurare da dama a lokacin zaben da aka kammala.

Ya kuma ce za su yi nazari tare da neman hanyar da za a bi wa ƴaƴan jam’iyyar na NNPP hakkinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here