Hukunce-hukuncen sallar idi da zakatul fidir

0
146

Zakatul fidr wato zakkar fidda kai sunnah ce mai karfi tana wajaba a kan kowanne musulmi babba da yaro mace dana miji da ko bawa da sharadin akalla sa’i guda ya ragu daga cikin abincin da mutum ya mallaka a ranar da ta wajaba a kansa.

Yawanta sa’i guda ne a kan kowanne mutum (Sa’i kuwa shi ne mudun nabiyi hudu ga kowanne mutum) lokacin take wajaba a kan wanne mutum shi ne da faduwar rana, a yinin karshe na Ramadan. A wani kauli kuwa an ce ba ta wajaba sai washe garin sallah.

Amma dai a kowanne hali sunnah ne a yi saurin fitar da ita da fitowar alfijir na ranar sallah.

Ana ba da ita ga musulmi fakiri ko miskini, kuma ba a bayar da ita ga bawa ko kafiri, da mawadacin mutum.

Mutum shi zai fitar da zakkar nan ga wanda ciyar da shi ta wajaba a kansa da sababin zumunta ko aure ko bauta.

Idan ta wajaba a kan mutum amma ya yi jinkirin fitar da ita to ba ta faduwa a kansa, saboda haka zai fitar da ita ko bayan watanni masu yawa. Ba ya halatta a fitar da ita sai daga daya daga cikin nau’in abincin nan:

  1. Alkama
  2. Sha’ir
  3. Sultu
  4. Dabino
  5. Zabib
  6. Cuku
  7. Gero
  8. Dawa
  9. Shinkafa
  10. Alasu
  11. Masara ko garin masara
  12. Wake
  13. Maiwa.

Amma idan an rasa daya daga cikin wadannan ya halatta a fitar da ita daga irin abincin da mutanen wajen suke ci.

Ita zakkatul fidr ya halatta a fitar da ita kafin kwana daya a yi sallah ko saura kwana biyu sallah, wani kaulin ma ta halatta ko da kafin kwana uku ne. Dan Annabi ya ce ita zakatul fidr tana kara tsarkake mai azumi da yawaita ladansa kuma ciyarwa ce da taiimako ga fakirai da miskinai wanda ya ba da ita kafin zuwa masallacin idi to tana da ladan zakka cikakkiya kuma karbabbiya amma wanda ya ba da ita bayan sauka daga sallar idi to sadaka ce daga cikin sadakoki. Wannan yana nuna mana ana son mutum ya yi gaggawar fitar da ita kafin sallar idi, amma ko da bayan sallar idi ne ba ta fadi ba a kan mutum sai dai idan ba shi da abin yi kwata-kwata, to a nan kam ta fadi a kansa. Dan Allah yana cewa “Ba ma dora wa rai abin da ba ta da iko a kansa” kuma Allah ya sake cewa “ku ji tsron Allah gwargwadon ikonku”.

An tambayi Annabi SAW a kan ayar nan da take cewa “hakika wanda ya tsarkake kansa ya rabauta ya kuma ambaci sunan Allah ya yi sallah saboda shi”. Annabi ya ce ai wannan aya ta sauka ne don tabbatar da zakatul fidr. Dan huzaima ya rawaito wannan hadisin.

Hukunce-Hukuncen Sallar Idi

Sallar idi sunnah ce mai karfi a kan kowanne namiji baligi da mai hankali, ba matafiyi ba, kuma abar so ce bisa yara maza da bawa da matafiyi da tsohuwar da ba a sha’awarta. Yawan sallar idi raka biyu ce. Babu bambanci tsakanin yadda aka yi sallar idin karamar sallah da ta babbar sallah.

Ga yadda akeyinta:

Tun farko mutum zai yi niyyar koyi da liman Ya ce “Na yi niyyar koyi da liman a cikin sallar idin kaza amma a boye a zuciyarsa ba a bayyane ba don fada a bayyane ba a samu a shari’a. Daga nan liman zai ce Allahu Akbar sau bakwai 7 a cikin raka’a ta farko, tun kafin ya fara karatu. Kabbarar haramar sallar tana cikin guda bakwai din. Shi kuma mai bin liman zai fadi “Alllahu Akbar” bayan fadar liman amma sau daya kawai ake daga hannu sama wato a wajen kabbarar farko.

Da kare kabbarorin nan sai liman ya karanci fatiha da surah a bayyane amma an fi son surar Sabbi a cikin raka’a ta farko. Sa’annan ya yi ruku’u da sujjadai sannan ya mike tsaye don yin raka’a ta biyu. Zai ce Allahu Akbar sau shida kafin ya fara karatu. Kabbarar mikewa tsaye tana cikinsu, zai karanta fatiha da sura a bayyane amma an fi son karanta Suratul Shamsu a cikin raka’a ta biyu, sannan ya yi ruku’i da sujjadai, ya zauna ya yi tahiya ya yi sallama.

Bayan kare sallah sai liman ya fuskanci jama’a ya yi huduba biyu. Zai zauna a farkonsa da tsakiyarsa, zai fara kowace huduba da kabbarori kuma ya yawaita fadarsu a hudubarsa wato misali zai dinga cewa “Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar” a lokacin nan dole ne wajibi ne mutane su yi shiru su saurari abin da yake fada a cikin hudubarsa.

Yadda Ake Gyaran Sallar Idi

Idan mutum ya samu liman yana tsakiyar karatu a cikin raka’a ta farko ko ta biyu sai ya yi niyya ya bi shi ya fadi kabbarorin nan bakwai ko shi kadai, idan kuwa ya riga ya samu liman ya yi wasu kabbarori sai ya bi shi ga sauran. Bayan liman ya cika nasa, shi kuma mai binsa sai ya kawo ragowar wanda bai samu yi da liman ba. Idan mutum ya tarad da liman yana ruku’u sai ya yi niyya ya sunkuya ga ruku’u dan ya same shi. Shikenan kabbarorin wannan raka’a sun fadi gare shi, babu komai a kansa, sallah ta yi kyau.

Idan mutum ya samu raka’a ta biyu tare da liman, idan zai rama ta farko zai yi mata kabbarorin nan nata bakwai 7. Idan Imam ya kara wasu kabbara a bisa adadin da aka iyakancen bisa mantuwa, mai koyi da shi ba zai fadi karin nan ba, idan liman ya rage kabbara daya ko abin da ya fi daya bai tuna ba sai bayan da ya yi ruku’i to shi ma zai yi sujjadar Kabli, idan kuwa kafin ruku’i ne sai ya fadi kabbarar sai ya sake karatu daga farko to zai yi kabbarar ba’adi. Idan mutum bai samu zuwa masallacin idi ba domin wani uzuri ko kuma da gangan to ana so ya yi kabbarorin nan shi kadai.

Sunnonin Idi

Sunnah ne mutum ya rayar da daren sallah da yawaita ibada ga Ubangiji Allah. Kamar sallar nafila da karatun Alkur’ani da Tasbihi. Kuma a ranar sallah abin so ne ga kowanne musulmi babba da yaro mace da namiji mai zuwa masallacin idi da wanda ba ya zuwa ya yi wanka, an fi so mutum ya yi wanka tun da asuba wato bayan fitowar alfijir, kuma ana iya yinsa ko da bayan fitowar rana.

Haka kuma abin so ne, ya sanya tufafinsa mafi kyau a ranar sallah. An fi son sababbin tufafi idan da hali, kuma abin so ne mutum ya tafi masallacin idi a kasa da gabobinsa, amma a wurin dawowa gida bayan ka gama sallah zai iya hawa duk abin da ya ga dama. Kuma abin so ce mutum ya sake sabuwar hanya a lokacin dawowarsa daga masallacin idi.

Abinso ne ga wanda zai tafi masallacin idi ya yi ta yin kabbara tun daga fitowarsa daga gida har isar sa masallaci kuma ya ci gaba da yin kabbarorin nan har sai lokacin da Imam ya tashi yin sallah. Ga yadda kabbarorin suke “Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, La ila ha illallah, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Wa lillahil hamdu”. Idan mutum ba zai iya fadar dukkan wadannan ba sai ya yi ta maimaita Allahu Akbar, Allahu Akbar ya isa. Kuma ba laifi yara su yi wasanni na farin ciki a ranar sallah.

Fadakarwa

Ba a sallar nafila idan aka isa masallacin idi saboda ita ma nafilace sai dai a yi ta Tasbihi har liman ya iso.

Wannan shi ne takaitaccen bayani dagaLittafin Alkalin Alkalai Alhaji Halliru Binji, Mai Suna “Ibada Da Hukunci A Addinin Musulunci”. Allah ya jikansa da gafara da mutanen gidansa da zuri’arsa da mu baki daya.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here