Yan bindiga sun kashe mutum 8 a kudancin Kaduna

0
132

Akalla mutane takwas ne aka kashe a garin Atak’Njei da ke Ungwa Gaiya a karamar hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna bayan wasu ‘yan bindiga sun kai wa al’ummar garin hari.

Atak’Njei a nan fadar al’ummar Atyap ta ke.

Duk da cewa har yanzu rundunar ‘yan sanda ko gwamnatin jihar ba su ce uffan ba kan harin ba, shugaban karamar hukumar Zango Kataf, Mista Francis Sani ya bayyana cewa maharan sun afkawa al’ummar ne da misalin karfe 9 na daren rabar Laraba.

A cewar majiyoyin al’ummar yankin, ‘yan bindigar sun kai hari a gidaje bakwai, inda suka harbe mutane takwas har lahira yayin da wasu da dama suka samu raunuka daban-daban.

A nasa jawabin, shugaban kungiyar ci gaban al’ummar Atyap (ACDA), Mista Sam Timbuwak Achie, ya yi tir da harin tare da bayyana shi a matsayin dabbanci.

Ya kuma dorawa duk wadanda ke da alhakin kare al’ummar yankin su yi abin da ya dace.

Idan dai za a iya tunawa, ‘yan makonnin da suka gabata ne ‘yan bindiga suka kashe akalla mutane 10 a yankin Langson da ke karamar hukumar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here