Za a fara ba duk matar da ta haihu miliyan 5 a Koriya ta Kudu

0
183

Sakamakon fama da karancin haihuwa a Koriya ta Kudu, kasar ta fara ba dukkan matanta da suka haihu tallafin Dalar Amurka 10,500, kwatankwacin sama da Naira miliyan biyar.

Hakan dai na zuwa ne yayin da kasar, wacce ita ce ta fi kowacce karancin haihuwa a duniya ta fara fuskantar barazanar raguwa.

Domin magance matsalar raguwar jama’ar ce gwamnatin kasar da ma na Jihohi suka kirkiro da tsare-tsare daban-daban da nufin karfafa wa matan kasar gwiwa su rika haihuwa.

Tun a shekara ta 2022 dai, duk matar da ta haihu takan sami tallafin Dalar Amurkar 1,510, tallafin da ya zarta hatta na kasar Faransa wacce ta fi shahara a fannin a duniya.

Kazalika, akan ba kowanne iyali tsabar kudi har Dalar Amurka 528 kowanne wata a kan kowanne jariri, har sai ya shekara daya cif, da kuma Dala 264 ga jarirai ’yan kasa da shekara biyu.

Ana sa ran kudin za su karu daga nan zuwa shekara ta 2024. kasar za kuma ta rika bayar da Dala 151 kowanne wata ga yara har sai sun kai matakin shiga firamare, sannan akan yi kari ga masu karamin karfi da matan da ba su da mazaje.

Sauran abubuwan tallafin da ake ba matan sun hada da biyan kudin asibiti kyauta ga mata masu juna-biyu, maganin matsalolin haihuwa, raino da kuma sauran kudaden ’yan kun-ji-kun-ji.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here