Atiku bai cika sharudan lashe zabe ba – INEC

0
127

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, bai cika sharudan da kundin tsarin mulkin kasar Najeriya ya gindaya ba na lashe zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.

INEC ta bukaci kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa da ta yi watsi da karar da Atiku da jam’iyyarsa suka shigar na kalubalantar sakamakon zaben.

Ta bayyana wa kotun cewa Atiku ya gaza samun akalla kashi daya bisa hudu na kuri’un da aka kada ko akalla kashi biyu bisa uku na jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, don haka babu yadda za a ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara.

INEC ta kara da cewa an gudanar da zaben ne bisa ka’ida da dokar zabe ta 2022 kuma dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu ne ya lashe zaben da kuri’u 8,794,726, inda ya doke Atiku wanda ya samu 6,984,520 a matsayi na biyu, sai Peter Obi na Jam’iyyar Labour wanda ya samu 6,101,533.

Atiku da Tinubu sun lashe jihohi 12 kowane yayin da Obi ya lashe jihohi 11 da birnin tarayya.

Atiku da Obi dai sun garzaya kotu i da suke kalubalantar ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben da INEC ta yi.

Amma INEC ta bayyana wa kotun cewa kundin tsarin mulki bai bai wa birnin tarayya  wani matsayi na musamman a kundin tsarin mulki ba kamar yadda wasu jam’iyyun siyasa da ’yan takarar da suka fadi zabe suke ikirari.

INEC ta ce dan takarar jam’iyyar APC ne ya cika dukkan sharudan da doka ta tanada na lashe zaben.

Ta yi nuni da cewa, ba dole ne dan takara ya samu kashi 25 cikin 100 na kuri’u a birnin tarayya ba kafin a ayyana shi a matsayin wanda ya ci zabe.

Hukumar ta bayyana cewa Tinubu na APC ya samu kashi 25 cikin 100 na yawan kuri’un da aka kada a jihohi 29 da ka yi zaben.

INEC ta kara da cewa ta bangaren shugaban kasa, ba ta yi gaggawar sanar da sakamakon zaben ba, kamar yadda Atiku da PDP suka yi zargi.

Ta ce Tinubu ya samu kashi 25 cikin 100 na kuri’un da aka kada a jihohi 29, don haka ta bukaci kotun da ta yi watsi da karar.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here