An gurfanar da tsohuwa a kotu kan laifin fashi a banki

0
176

Ƴan sanda sun ce sun sake kama wata tsohuwa mai shekara 78 bisa zargin ta da yin fashi a wani banki a jihar Missouri.

Dama dai an taɓa kama tsohuwar da laifukan yin fashi a banki sau biyu a baya.

Bonnie Gooch ta shiga bankin Goppert Financial Bank, inda aka yi zargin ta miƙa wa masu bayar da kuɗi takarda, tana umurtar sa ya ba ta dubban daloli.

Sannan ta ajiye wata takarda mai ƙunshe da cewa “Na gode, ku yi haƙuri, ban so na tsorata ku ba” kafin ta ja motarta ta tafi da kuɗin.

A yanzu haka dai Ms Gooch tana tsare a gidan maza.

Takardun da aka gabatar wa kotu sun nuna cewa, Ms Gooch sanye da baƙaƙen kaya da takunkumi da safar hannu, ta shiga cikin bankin ne a ranar Larabar makon jiya, inda ta zura wa mai bayar da kuɗi wata takarda ɗauke da saƙon da ke cewa “Ina buƙatar 13,000”.

Bidiyon da kyamarar tsaro ta ɗauka ta nuno matar a wani lokaci tana buga kan teburi tana buƙatar mai bayar da kuɗi ya hanzarta.

Bayan amsa kiraye-kirayen ankarar da jami’an tsaro kan fashi da makami, ƴan sandan garin Pleasant Hill, a jihar Missouri, sun gano Ms Gooch a cikin motarta tana warin barasa da kuɗi baje a ƙasa, in ji mai gabatar da ƙara.

An kama ta tare da gurfanar da ita gaban kotu bisa zargin sata da kuma ƙoƙarin yin fashi a banki.

“Lokacin da ƴan sanda suka dumfari inda take, sun shiga ruɗani …ganin cewa wata tsohuwa ce ta fito,” in ji babban jami’in ɗan sanda na Pleasant Hill, Chief Tommy Wright.

Sai dai wannan ba shi ne karon farko da ake gurfanar da Ms Gooch a kotu ba.

An taɓa kama ta da laifuka biyu.

Na farko shi ne laifin fashi da makamai a California cikin shekarar 1977, na biyu kuma shi ne fashin banki a 2020, inda a lokacin ta miƙa wa mai bayar da kuɗi a banki wani kati irin na murnar zagayowar ranar haihuwa, sai dai yana ƙunshe ne da rubutun da ke cewa “na zo yin fashi.”

Mr Wright ya ce bayanai sun nuna cewa Ms Gooch ba ta fama da wani rashin lafiya, sai dai ya ce za su ƙara bincikawa ko tana da wata cutar da ba a sani ba, wadda ke tunzura ta yin irin wannan aika-aika, ta yin la’akari da shekarunta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here