Adam A Zango ya saki matar sa ta shida

1
713

A karshe dai shahararren mawaki kuma furodusa a masana’antar finafinai ta Kannywood, Adam A. Zango, ya saki matarsa, Safiya Umar Chalawa.

Jarumin ya sake ta ne shekara hudu bayan aurensu da aka daura a 2019 a Fadar Sarkin Gwandu a Jihar Kebbi.

Da haka ne Safiyya ta zama matarsa ta shida da ya saka a cikin shekaru 17 da suka gabata, daga 2006 zuwa yanzu.

Adam A. Zango, wanda ya yi tashe a Kannywood, yana da ’ya’ya bakwai, kowanne daga cikinsu mahaifiyarsa daban, in banda biyu daga cikinsu.

A kwanakin baya Aminiya ta ruwaito cewa Adam A. Zango na dab da rabuwa da amaryarsa Safiya, wadda aka ji shi a wani bidiyo yana zargin cewa ta zabi kasuwancinta a kansa.

A cewarsa, hakan ne ya sa ba shi da wani zabi face ya hakura da ita, kuma idan ya rabu da ita ba zai kara yin aure ba.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here