Abin da kuke son sani kan wasan Real da Chelsea a Champions

0
159

Real Madrid da Chelsea za su buga wasan farko zagayen quarter finals a Champions League a Santiago Bernabeu ranar Laraba.

Real ta kawo wannan matakin, bayan da ta fitar da Liverpool da cin 6-2 gida da waje a kakar bana.

Ita kuwa Chelsea ta yi nasarar yin waje da Borussia Dortmund da cin 2-1 gida da waje.

Kungiyoyin sun kara a bara a Champions League, inda Karim Benzema ya ci kwallo hudu, wanda Real ta yi nasara da cin 5-4.

Real tana da Champions League 14, kociyanta Carlo Ancelotti ya lashe hudu a matakin mai horar da tamauala, wanda zai fuskanci tsohuwar kungiyarsa.

Da yake Barcelona ce take ta daya a La Liga da tazarar maki 13 tsakaninta da Real Madrid, kungiyar Santiago Bernabeu ta mayar da hankali kan sake lashe kofin nan na Champions League.

Chelsea kuwa wadda ba ta kokari a kakar nan, wadda ta kori Thomas Tuchel da Graham Potter – yanzu ta sake bai wa Frank Lampard kungiyar aikin rikon kwarya zuwa karshen kakar nan.

Chelsea tana mataki na 11 a teburin Premier League, da kyar idan za ta samu gurbin ‘yan hudu a bana, saboda haka lashe Champions League ya zama wajibi a gareta, idan ba haka ba za ta buga gasar zakarun Turai ba a badi.

Vinicius Junior na Real Madrid ya zura kwallo shida a raga a Champions League na bana, shine kan gaba a kungiyar a kakar nan.

Chelsea tana da Champions League biyu, ita kuwa Real ita ce mai rike da na bara kuma na 14 jimilla.

‘Yan wasan Real da za su kara da Chelsea:

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da Luis López.

Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Lucas V. da Rüdiger.

Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni da D. Ceballos.

Masu cin kwallaye: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr., Rodrygo da Mariano.

Wasa tsakanin Real Madrid da Chelsea

2021/2022 Champions League

  • Real Madrid 2 – 3 Chelsea
  • Chelsea 1 – 3 Real Madrid

2020/2021 Champions League

  • Chelsea 2 – 0 Real Madrid
  • Real Madrid 1 – 1 Chelsea

1998/1999 European Super Cup

  • Chelsea 1 – 0 Real Madrid

1970/1971 Euro Cup Winners Cup

  • Chelsea 2 – 1 Real Madrid
  • Chelsea 1 – 1 Real Madrid.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here