‘Yan bindiga sun kashe sojoji a Jamhuriyar Nijar

0
130

‘Yan bindiga sun kashe sojoji akalla biyar a Jamhuriyar Nijar a yankin da ake hakar gwal da ke kusa da Aljeriya.

Bayanai sun nuna cewa sojojin suna gadin tawagar masu hakar gwala-gwalai ne.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa ‘yan bindidar sun saje da tawagar inda suka bude wuta kan sojojin a ranar Lahadi.

Sojojin sun bi ‘yan bindigar da gudu amma suka “fada wurin da aka yi musu kwanton-bauna lamarin da ya yi sanadin mutuwar biyar daga cikinsu”, a cewar wata majiya.

Tawagar tana kan hanyarta ta zuwa garin Arlit daga wurin hakar gwal na Tchibarakaten mai nisan kilomita 450 daga area maso gabashin kasar inda dubban mutane suke hakar gwala-gwalai.

Wani da ya sha da kyar daga harin ‘yan bindigar ya shaida wa jaridar Air Info da ke yankin Agadez cewa maharan da suka yi wa sojoji “kwanton-bauna” suna dauke da “muggan makamai”.

Jaridar ta ce sojoji biyar ne suka jikkata sakamakon harin.

Wani shugaba a yankin ya gaya wa AFP cewa watalika ‘yan bindigar sun samu labarin tawagar kuma “mai yiwuwa sun kwace gwala-gwalai da dama” daga wurinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here