Sojoji sun kashe wani fitaccen ɗan bindiga a Kaduna

0
123

Gwamnan jihar Kaduna da ke arewa maso yammaci Najeriya Malam Nasir El-Rufai ya jinjina wa dakarun sojin ƙasar da ke aiki a jiharsa, kan kisan wani fitaccen ɗan fashin daji mai suna Isiya Danwasa.

A cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar, ya ce dakarun sojin sun kashe ɗan fashin dajin a yankin sabon birni na ƙaramar hukumar Igabi da ke jihar.

Isiya Danwasa dai fitaccen ɗan fashin daji ne da ya addabi jihar da satar mutane domin neman kuɗin fansa, da fashi da kuma satar shanu.

Daga ƙarshe gwamnan ya yi kira ga mazauna jihar da su ci gaba da bai wa jami’an tsaron sahihan bayanai da za su fallasa ɓata-garin.

A nasu ɓangare kuma jami’an sojin Najeriya da ke aiki a ƙarƙashin rundunar Operation FOREST SANITY da ake Kaduna tare da haɗin gwiwwar dakarun shalkwatar rundunar tsaro ta ƙasar sun ce sun kama wani yaron jagoran ‘yan fashin daji a garin Mando a yankin ƙaramar hukumar Igabi.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafin na Tuwita ta ce jami’anta sun kama yaron ‘yan fashin ne a lokacin da ubangidan nasa ya aike shi domin sayen harsasai a cikin gari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here