An sayar da tikiti 650,000 kwana 100 kafin fara gasar Kofin Duniya ta mata

0
169

Masu shirya gasar Kofin Duniya ta mata da za a fara nan da kwana 100, sun ce suna sa ran sayar da tikitin kallon gasar kimanin miliyan ɗaya da rabi wani abu da ba a taɓa gani ba a tarihin gasar.

Kawo yanzu an sayar da tikiti 650,000 na gasar da hadin gwiwwar ƙasashen Australia da New Zealand za su karɓi baƙunci.

Sakatariyar hukumar FIFA Fatma Samoura ta ce ”manufar FIFA ita ce a wannan shekarar ta shirya gasar Kofin Duniya ta mata mafi girma a tarihin duniya”.

Za a fara gasar ne ranar 20 ga watan Yuli, inda za a kammala gasar ranar 20 ga watan Agusta.

Hukumar FIFA ta kuma yi hasashen cewa za a samu kallon gasar a talbijin kusan biliyan biyu.

FIFa ta ce fatan samun masu kallo fiye da 100,000 da za su halarci bikin buɗe gasar a wasan da New Zealand za ta kara da Norway.

A gasar 2019 da ta gabata a Faransa, FIFA ta sayar da tikiti 720,000 kwana 50 gabanin fara gasar, inda a gaba ɗayan gasar aka sayar da tikiti 950,000.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here