‘Yan sa-kai sun kashe makiyaya 12 a Sokoto

0
165

Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetta Allah a Najeriya ta yi shelar cewar ‘Yan sa-kai a jihar Sokoto sun halaka mambobin ta 12 sakamakon wani farmakin da suka kai matsugunansu da ke yankin Gwadabawa.

ke fama da matsalar ‘yan bindiga barayin shanu, abinda ya sa wasu al’ummomi suka kafa kungiyoyin Sa-kai domin taimakawa jami’an tsaro kare lafiya da dukiyoyin jama’a.

Lokaci zuwa lokaci ana samun arangama tsakanin Fulani makiyayan da ‘Yan sakai abinda ke kaiga rasa rayuka.

Shugaban kungiyar Fulanin na kasa Baba Usman Ngelzerma ya bukaci gwamnati da ta tashi tsaye wajen dakile wannan matsala da kuma hukunta duk wadanda aka samu suna da hannu a ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here