Cutukan da suka kamata a yi taka-tsantsan da su lokacin azumi

0
101

Al’ummar Musulmi a faɗin duniya na ci gaba da azumtar watan Ramadan domin ibada ga mahaliccinsu.

Azumi na nufin daina cin abinci da abin sha, da kusantar iyali daga ketowar alfijir zuwa faɗuwar rana da nufin neman yardar Ubangiji.

To sai dai kamar yadda likitoci suka yi bayani akwai wasu cutuka da ke tasowa, ko suna iya ƙara muni a lokacin azumi sakamakon daina cin abinci a tsawon wuni.

Haka kuma a gefe guda likitocin sun ce akwai wasu cututtuka da ake samun sauƙi musamman a lokacin azumin.

Dakta Mu’awiya Aliyu ma’aikaci a hukumar lafiya ta jihar Katsina ya ce a lokacin azumi akwai cututtuka da ka iya tashi kamar:

Gyambon ciki

Cuta ce da ke sanya cikin mutum ya yi ta zafi kamar an barbaɗa borkono.

”Hakan na faruwa ne saboda ƙarancin abinci a cikin mutum, kuma mai ɗauke da cutar zai riƙa jin tana tashi a lokacin da bai ci abinci ba”, in ji Dakta Mu’awiya.

Cutar ƙoda

Dakta Mu’awiya ya ce akwai wasu cutakan da ke shafar ƙoda, waɗanda rashin shan ruwa ke haddasa su.

Likitan ya ce masu irin wannan cuta, akan ba su shawara, su riƙa yawan shan ruwa a kai-a kai.

Cutar mafitsara

Ita ma wannan cuta ce da ke bukatar yawan shan ruwa kasancewa ruwan kan taimaka wajen wanke ciwon da ke damun mafitsarar.

Wasu cutuka da ke janyo taruwar duwatsu

A cikin ƙodar mutum ko mafitsara, su ma waɗannan cutuka akan buƙaci mai fama da su ya riƙa yawan shan ruwa wanda zai taimaka wajen narkar da duwatsun.

Likitan ya ce ”irin waɗannan cutuka su ma suna yawan tashi musamman a lokacin azumi”.

Haka kuma Dakta Mu’awiya ya ce akwai cutar Matsarmama wadda ita ma ke buƙatar yawan shan ruwa.

Cutakan da ake samun sauƙinsu a lokacin azumi

Haka kuma, likitan ya zayyana wasu cutuka da ya ce ana samun sauƙin tashinsu musamman a lokacin azumi.

Cutukan zuciya

Likitan ya ce da ma mafi yawan abin da ke haddasa cutukan zuciya su ne yawan kitse da maiƙo a jikin zuciyar.

Cutar kansa

Wasu dalilan cutar, su ne girma na wuce kima da wani ɓangare na jikin mutum ke yi, ”to a wannan yanayin da mai cutar ke azumi, to ka ga babu abincin ma da mutum zai ci balle cutar ta habaka”, in ji likitan.

Cutar amai da gudawa

Likitan ya ce ”Da ma ta hanyar cin wani nau’in abinci da ya gurɓata ko ya cuɗanya da ƙwayar cutar ne ake samun amai da gudawa, to amma idan ana azumi, (ai) ba a ma ci abincin ba, balle a ci ƙwayar cutar”.

Cutar hanta

Hanta ita ce ke tace duk wani abinci domin fitar da abubuwa marasa amfani da mutum ya ci, kamar yadda Dakta Mu’awiya ya bayyana.

Ya kuma ce ”idan mutum na azumi hantarsa za ta samu sauƙin aiki, to a nan hantar kan samu sauƙi sosai a lokacin da babu abincin da hantar za ta tace”.

Cutar ƙiba

Likitan ya ce ƙiba ma cuta ce, inda kitse yake taruwa a cikin tumbin mutum, ko ƙirjinsa ta yadda zai rufe zuciya ko ƙodar mutum.

A cewarsa, azumi yakan taimaka wajen rage ƙibar kasancewar lokacin cin abincin mutum ya zama ƙayyadajje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here