Bikin Ista: Yesu zai iya dawowa a kowane lokaci daga yanzu – Rabaran Mati

0
84

A yau ne mabiya addinin kirista a kasashen duniya ke gudanar da bikin Easter Monday, don tunawa da tashin Yesu Kiristi daga matattu, kamar yadda mabiya addinin suka yi imani.

Kiristocin na gudanar da bukukuwan ne bayan kammala addu’o’i tare da juyayin tunawa da ranar da aka bayyana cewa Romawa sun gicciye Yesu a juma’ar da ta gabata.

Rabaran Murtala Mati Dangora shi ne limamin cocin Ecwa da ke jihar Kano, a tattaunawarsa da BBC ya ce Easter Monday ranar murna ce da ya kamata kowane Kirista ya martaba.

Ya ce tashin da Yesu Almasihu ya yi daga matattu wani tabbaci ne da ke nuna cewa akwai ranar da duk wani É—an adam da ya mutu zai tashi.

Yaushe ne Yesu zai dawo?

A lokacin da aka tambayi Rabaran Mati ko yaushe ne Yesu Almasihu zai dawo? Sai ya ce duk wasu alamu da Yesu ya bayyana na kusantowar lokacin dawowarsa sun riga sun bayyana.

Ya ce “Almajiransa (Yesu) sun masa tambaya cewa yaushe ne za ka dawo? Mene ne kuma alamu na Æ™arshen zamani?

Rabaran Mati ya ce alamomin ƙarshen zamani da Yesu ya bayyana su ne:

  • Ƙauna ta mutane za ta yi sanyi
  • Za ka ga ana yaÆ™i tsakanin Æ™asa da Æ™asa
  • Zaman lafiya zai yi Æ™aranci
  • Za a riÆ™a yin rigima tsakanin uwa da Æ´a, tsakanin uba da É—ansa

Sai dai Rabaran Mati ya ce Yesu bai faÉ—i takamaiman rana da lokacin da zai dawo duniya ba.

Amma Rabaran É—in ya ce waÉ—annan alamu su ne suka nuna cewa Yesu Almasihu ya kusa dawowa.

“Babu wani alamu na Æ™arshen zamani da Yesu ya faÉ—a waÉ—anda ba su tabbata ba, domin haka muna jira ne ko yau ko gobe, kowace rana mai zai iya dawowa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here