Benzema zai tsawaita zama a Real Madrid, AC Milan na son Balogun

0
151

Tsohon kocin Leeds Jesse Marsch ya yanke shawarar ƙin karɓar aikin Leicester City, duk da yake, suna gab da kammala tattaunawa kan kwanturagin aiki da shi. (Telegraph)

AC Milan ta sanya sunan ɗan gaban Ingila, da ke bugawa rukunin ƙasa da shekara 21 Folarin Balogun, wanda ke matsayin aro a Reims daga Arsenal cikin jerin ‘yan wasan da take son ɗauka cikin sabuwar kakar wasanni, duk da yake tana jin Gunners ɗin na iya neman sama da yuro miliyan 30 a kan ɗan wasan. (Calciomercato – in Italian)

Tottenham ta nuna sha’awar ɗaukar ɗan wasan gefe na Moroko, Hakim Ziyech, mai shekara 30, daga Chelsea kafin kakar wasa mai zuwa. (Football Insider)

Manchester United na bibiyar ɗan wasan tsakiyar Celta Vigo, ɗan ƙasar Sifaniya, Gabri Veiga mai shekara 20, kafin yiwuwar ɗaukar sa a kaka mai zuwa. (Football Insider)

Manchester United ɗin dai ta sa sunan ɗan wasan tsakiyar Brighton, daga ƙasar Eucador, Moises Caicedo mai shekara 21, da ɗan wasan tsakiyar Argentina Alexis Mac Allister, mai shekara 24, cikin jerin ‘yan ƙwallon da take son ɗauka nan gaba. (Telegraph )

Tsohon ɗan wasan gaban Faransa, Karim Benzema, mai shekaru 35, yana son ci gaba da zama a Real Madrid tsawon a ƙalla kakar wasa ɗaya, bayan ya ƙi amsa tayin da aka yi masa daga ƙasar Saudiyya. (Marca – in Spanish)

Chelsea da Liverpool na harin ɗan wasan Inter Milan, Nicolo Barella, daidai lokacin katafaren kulob ɗin na Italiya ya shirya sayar da ɗan ƙwallon tsakiyar na ƙasar Itali mai shekara 26 a kan kuɗi fam miliyan 44. (Calciomercato, via Sun)

Manchester United ta yi tattaunawa mai armashi da Monaco a kan yiwuwar ɗaukar ɗan wasan bayan Faransa, Axel Disasi, mai shekara 25. (Give Me Sport)

Manchester United na iya mayar da hankali wajen ɗaukar ɗan bayan Bayern Munich daga ƙasar Faransa Benjamin Pavard mai shekara 27, matuƙar babbar ƙungiyar ta ƙasar Jamus ta riga United a wajen sayen ɗan bayan Bayer Leverkusen ɗan ƙasar Holland Jeremie Frimpong mai shekara 22 kafin kakar wasanni mai zuwa. (Football Insider)

Golan Sifaniya David Raya ba zai sa hannu kan wata sabuwar yarjejeniya da Brentford ba, ƙungiyar da ke neman kulob ɗin da zai biya yuro miliyan 40 don ɗaukar ɗan wasan mai shekara 27 a wannan bazara. (Fabrizio Romano)

Bologna da Leicester City na zawarcin ɗan wasan tsakiyar a , ɗan ƙasar Wales, Jordan James mai shekara 18. (Sun)

Ɗan wasan tsakiya na Faransa Adrien Rabiot, mai shekara 28, ya ce har yanzu yana dakon tattaunawa a kan ko zai cimma sabon kwanturagi da Juventus. Yarjejeniyar aikinsa ta yanzu dai na gab da ƙarewa a bazara. (Fabrizio Romano)

Ɗan wasan Borussia Dortmund Marco Reus, wanda kwanturaginsa zai ƙare a wannan bazara, ya shirya rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya a kaka wasanni mai zuwa, duk da yake sai an daddale kan batun rage wa ɗan wasan na Jamus mai shekara 33 kuɗi. (Bild – in German)

Koci Xavi Hernandez zai dage a kan cewa Sergio Busquets sai ya ci gaba da zama a Barcelona a ƙalla tsawon kakar wasa guda, kafin ɗan wasan tsakiyar na Sifaniya mai shekara 34 ya bar ƙungiyar don koma wa wani kulob a Gasar MLS ta Amurka club. (Goal)

Sau biyu Real Madrid ta yi yunƙurin ɗaukar sabon manajan Chelsea na riƙo wato Frank Lampard, lokacin da tsohon ɗan wasan tsakiyar Ingilar mai shekara 44 ke kan ganiyar ƙwallonsa a tsakanin shekarun 2005 da 2010. (Mundo Deportivo – in Spanish)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here