Abin da kuke son sani kan wasan Barca da Girona

0
170

Barcelona za ta kara da Girona a La Liga wasan mako na 28 da za su fafata ranar Litinin a Camp Nou.

Barcelona za ta buga wasan bayan da Real Madrid ta fitar da ita a Copa del Rey, bayan doke ta 4-0 a Camp Nou.

To sai dai Barcelona tana mataki na daya a kan teburin La Liga da tazarar maki 12 tsakaninta da Real Madrid ta biyu mai rike da kofin bara.

Girona mai maki 34 tana ta 11 a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya, bayan karawa 27.

Girona birni ne na kwararrun masu wasan tseren kekuna da hada fina-finai – birnin ya dade a fannin tamaula a rukuni na biyu da na uku a gasar tamaula ta Sifaniya.

Ya fara buga gasa mai daraja ta biyu a Sifaniya a 2008 daga nan ya samu gurbin shiga La Liga a 2017.

Kaka biyu Girona ta yi a La Liga daga nan ta yi shekara uku a rukuni na biyu daga baya ta koma buga La Liga a kakar da ta wuce.

Karawa tsakanin Barca da Girona

Kungiyoyin biyu sun kara a bana ranar 28 ga watan Janairu, inda Barcelona ta je ta ci 1-0, Pedri ne ya ci mata kwallon a minti na 61.

A wasa hudu baya da suka kara a lokacin da Girona ke buga La Liga, Barca ce ta yi nasara a uku, yayin da Girona ta buga 2-2 a Camp Nou.

Bayani kan tsare baya a bana a La Liga tsakanin kungiyoyin:

Kwazon da Barca ke yi a bana ya kunshi kwazon masu tsaron bayanta, wadda ta buga karawa 20 kwallo bai shiga ragarta daga wasa 27 a La Liga a bana.

Ita kuwa Girona wasa daya ne ta yi kwallo bai shiga ragarta ba a kakar nan, shine wanda ta yi nasara a gida da cin Valencia 1-0.

Kwallo 42 Girona ta zura a raga, ita kuwa Barcelona 53 ta ci, Real ce kan gaba mai 59 a La Liga a kakar nan.

Kociyan Girona:

Miguel Angel Sanchez Munoz, wanda ake kira Míchel, ya taka leda a Rayo Vallecano, sannan ya horar da kungiyar tamaula.

Bayan da ya ja ragamar Huesca, ya karbi aikin horar da Girona a 2021, wanda ya kai kungiyar La Liga.

Michel ya fuskanci Barça karo hudu a matakin kociya, wanda ya yi rashin nasara biyu a Rayo da wanda Barca ta yi nasara a bana a Girona da wanda aka doke shi a Huesca.

‘Yan wasan da suka yi kungiyoyin biyu:

‘Yan wasa hudu ne a Girona da suka yi Barcelona a baya.

Mai tsaron bayan Uruguayan, Santi Bueno ya buga wa matasan Barca a 2017 da kungiya ta biyu.

Arnau Martínez da Valery Fernández sun taka leda a La Masia, kafin su koma taka leda a Girona.

Oriol Romeu shine wanda kowa zai fi tunawa, mai buga tsakiya ya yi Barca daga 2004 zuwa 2011.

Daga nan ya koma Chelsea ya kuma buga wasa sama da 200 a Southampton.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here