A karon farko mace da wani baƙar fata za su tafi duniyar wata (Hotuna)

0
97

Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka (NASA) ta bayyana sunan ‘yan sama jannati hudu da za su koma duniyar wata, bayan tsaikon shekara 50.

Christina Koch za ta zama mace ta farko ‘yar sama jannati da za ta je duniyar wata, yayin da shi kuma Victor Glover zai zama baƙar fata na farko ɗan sama jannati a tafiyar.

Za su tafi tare da Reid Wiseman da Jeremy Hansen waɗanda za su tuƙa su zuwa duniyar watan ƙarshen shekara gobe ko kuma farkon 2025.

‘Yan sama jannatin ba za su sauka a duniyar wata ba, amma shirinsu zai buɗe hanya ga waɗanda za su tafi a nan gaba su samu wajen sauka.

An gabatar da ‘yan Amurka uku da ɗan Canada ɗaya a gaban jama’a a matsayin waɗanda za su yi tafiyar a yayin bikin da aka yi a Houston da ke Texas.

Yanzu za su fara wani atisaye na musammam domin shiri ga tafiyar.

Zaɓen matar da wannan baƙar fata, wani bangare ne na cika alƙawarin da Nasa ta ɗauka na buɗa damar zuwa saman ga mutane daban-daban.

Duka mutanen da suka je a baya fararen fata ne kuma maza.

Reid Wiseman mai shekara 47: Wani Sojin ruwan Amurka ne da ya yi aiki a lokacin a matsayin shugaban ofishin ‘yan sama jannati na Nasa.

Ya taba zuwa saman a bya, zuwa wata tasha da ke saman a 2015.

Victor Glover mai shekara 46: Dan Amurka ne matuƙin jirgin saman ruwa. Ya koma Nasa a 2013, ya kuma fara ta shi zuwa sama ne a 2020. Shi ne baƙar fata na farko da ya fara kwashe wata shida a tashar sama.

Christina Koch ‘yar shekara 44: In ji niya ce: ita ce ta kafa tarihin macen da ta fi daɗewa a sararin samaniya inda ta shafe kwana 328. Tare da yar sama jannati ta Nasa Jessica Meir tana cikin mata na farko da suka yi tafiya a samaniya a Okotban 2019.

Jeremy Hansen mai shekara 47: Kafin komawa hukumar sararin samaniya ta Canada, matuƙin jirgin yaƙi ne tare da dakarun Royal Canada. Har yanzu bai taɓa zuwa samaniya ba.

“Tawagar Artemis-2 za ta wakilci dubban mutanen da ke aiki ba dare ba rana domin su kaimu ga taurari. Wannan ce tawagarsu, kuma ita ce tawagarmu, tawagar mutane kenan,” in ji Bill Nelson shugaban gudanarwar Nasa.

“Reid Wiseman da Victor Glover da kuma Christina Hammock Koch yan sama jannatin Nasa ne, sai Jeremy Hansen dan sama jannatin Canada ne, dukkansu za su wakilci imaninmu.

Wiseman shi ne zai zama jagoran tafiyar; Glover kuma zai tuƙa shi, Koch da Hansen za su zama masu taimakawa wajen ganin komai ya tafi daidai.

Tawagar za ta maimaita abin da Apollo 8, ta yi a 1968, wanda shi ne zuwan bil’adama na farko duniyar wata.

Tawagar ta ɗauki yadda rana take fitowa zai nuna yadda rana ke fitowa daga bayan duniyar wata.

Babban banbancin da za a samu zai zama amfani da sabuwar fasahar da Nasa ta samar a ƙarni na 21 ƙarƙashin shirinta na Artemis. A yaran Greek Artemis na nufin Apollo mai guda biyu.

A bara ne hukumar ta gwada kumbonta da za a je duniyar wata da shi nan gaba, wanda aka kira SLS amma aka fi sani Orion.

Shi wannan Artemis-1 din ya bar duniya kwana ashirin da biyar zuwa duniyar wata babu kowa cikin. hakan dai zai bai wa injiniyoyin damar shiri na gaske kan matakinsu na gaba.

Sabbin ‘yan sama jannatin da aka bayyana sunansu za su hau Orion na Artemis-2 wata tafiya da za ta iya ɗaukar kwana 10 zuwa da dawowa.

Jirgin ‘yan sama jannati na ƙarshe da yaje duniyar wata shi ne Apollo 17 a watan Disambar 1972. Wanda kuma ya fara sauka a duniyar shi ne Apollo 11 a 1969.

Artemis-3, na sabuwar fasahar da zai sauka, ba a sa ran zai fara aiki sai nan da aƙalla wata 12 bayan Artemis-2.

Nasa har yanzu ba ta ƙara kumbon da zai ɗauki ‘yan sama jannati ba zuwa dandagaryar duniyar wata. Kamfanin ɗan kasuwar nan ne kawai Elon Musk ya iya samar da wannan kumbo mai suna SpaceX.

Za a fara gwada abin hawan nan da makonni masu zuwa.

“Akwai buƙatar mu yi farin ciki da wannan lokaci a tarihin ɗan adam, Artemis-2 zai iya zuwa duniyar wata ya kuma dawo. wani shiri ne da za mu ƙaddamar gabanin aika mutane su sauka a dandagaryar duniyar wata. wannan ita ce tafiya ta gaba da mutane za su yi zuwa Mars,” in ji Victor Glover.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here