Wadanda suka sace mutum 100 a Zamfara na neman miliyan 60 a matsayin kudin fansa

0
128

Yan bindigar da suka sace mutum 100, ciki har da kananan yara guda 80 a Jihar Zamfara, sun bukaci a ba su Naira miliyan 100 kafin su sake su.

Wata majiya daga daya daga cikin iyalan wadanda lamarin ya shafa ne ya shaida wa Aminiya hakan ranar Asabar.

Maharan dai, wadanda ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne domin neman kudin fansa sun sace mutanen ne a tsakanin Jihohin Zamfara da Katsina ranar Alhamis.

Wani mazaunin kauyen Wanzamai da ke Karamar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara, wada ya ce sunansa Sani Wanzami, ya ce an kashi akalla mutum 80 a kauyensu, sai kuma wasu 20 a kauyukan da ke da makwabtaka da su.

“Maharan sun kira wasu daga cikin iyalan wadanda aka sace a waya, inda suka bukaci a biya su Naira miliyan 60 kafin su saki yaran. Tuni ha an fara tattaunawa, kuma har sun yi ragi yanzu sun mayar da kudin miliyan 30. sun bukaci ’yan uwan mutanen su je su yi tunani a kai,” in ji majiyar.

To sai dai Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Kolo Yusuf, ta bakin Kakakin rundunar a Jihar, CSP Muhammad Shehu, ya bayar da tabbacin cewa jami’ansa tare da hadin gwiwar ragowar jami’an tsaro na kokarin ganin sun ceto mutanen lami lafiya.

Ya ce tuni wata kakkarfar tawagar jami’an tsaron ta fara aikin sintiri da nufin ceto mutanen daga hannun maharan.

Kakakin ya kuma ce tuni Kwamishinan ya bayar da umarnin tura wata runduna ta musamman don ganin aikin ya sami nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here