Messi ya zarce Ronaldo a cin ƙwallaye a lik ɗin Turai

0
157

Lionel Messi ya ci ƙwallo na 702 a lik ɗin Turai, bayan Paris St Germain ta je ta doke Nice 2-0 a wasan mako na 30 na Ligue 1 ranar Asabar.

Minti na 26 da fara wasa, Messi ya ci ƙwallo, sannan Sergio Ramos ya ƙara na biyu, saura minti 14 a tashi wasan.

Da wannan sakamako, PSG ta ci gaba da jan ragamar teburin babbar gasar tamaula ta Faransa da maki 69, da tazarar maki shida tsakaninta da Lens ta biyu.

Tun bayan komawa PSG daga Barcelona a 2021, Messi ya bayar da ƙwallo 32 aka zura a raga, shi ne ya bai wa Ramos ya ci na biyu a ranar Asabar

A kakar nan Messi, wanda ya ci ƙwallo 14 a Ligue 1, ya kuma bayar da 14 aka zura a raga bana.

Kyaftin ɗin na Argentina ya ba da ƙwallo 269 aka zura raga a Barcelona, a watan jiya yayin karawa da Brest ya bayar da ta 300 wadda Kylian Mbappe ya ci.

Tun komawar Messi kulob ɗin PSG, kawo yanzu ya ci ƙwallo 30, ya kuma ba da 32 aka zura raga a dukkan fafatawa.

Messi ya buga wa Barcelona wasa 778 da cin ƙwallo 672 – ya koma Paris St Germain a 2021, kawo yanzu ya zura ƙwallo 30 a raga.

Ƙwallo 11 ya ci a PSG bara a dukkan fafatawa, inda a bana yake da 19 kawo yanzu.

Ƙwallayen da Ronaldo ya ci a ƙungiyoyin Turai:

Ƙungiya wasa Ƙwallo

Manchester United 346 145

Juventus 134 101

Real Madrid 438 450

Sporting 31 5

Ronaldo ya sha gaban Messi wajen cin ƙwallaye a tawaga 

Kyaftin Messi ya ci wa Argentina ƙwallo 102 a wasa 174 da ya buga mata, shi ne na uku a jerin waɗanda suka ci wa ƙasarsu sama da 100.

Ronaldo ne kan gaba, wanda ya buga wa Portugal wasa 198 da ƙwallo 122.

Ɗan ƙasar Iran Ali Daei shi ne na biyu, mai 109 a raga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here