Iran za ta sa kyamara a ko’ina don kama matan da ba sa yawo da hijabi

0
133

Hukumomin Iran sun fara kafa kyamarori a wuraren da mutane ke taruwa domin gano matan da ke yawo ba tare da hijabi ba, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana.

Duk macen da aka samu ba ta sanya hijabi ba za a “aika mata saĆ™on jan kunne,” in ji ‘yan sanda.

Wanda haka a cewarsu “zai rufe bakin masu adawa da wannan doka”.

Zanga-zanga ta mamaye Iran a bara, bayan an zargi ‘yan hizba da sanadin mutuwar wata matashiya mai suna Mahsa Amini, wata BaĆ™urdiya da aka zarga da karya dokar sanya hijabi.

Tun bayan mutuwar Mahsa, mata da yawa ke sanya hijabi musamman waÉ—anda ke zaune a manyan birane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here