Home Labarai Labaran Duniya Ana hasashen tafka ruwan sama a sassan Saudiyya har karshen Ramadana

Ana hasashen tafka ruwan sama a sassan Saudiyya har karshen Ramadana

0
131

Jaridar Saudi Gazette ta kasar ta ruwaito cewa ana sa ran soma wannan ruwa ne tun daga ranar Lahadi har zuwa karshen watan Ramadana.

Hukumar ta ce guguwa mai dauke da kura da ruwan sama mai karfi da kankara za su yi tsanani tun daga Litinin zuwa Alhamis a yankunan Qassim da Riyadh da Gabashin Saudiyya da kuma birnin Ha’il.

A sanarwar da hukumar da ke kula da hasashen yanayin ta fitar, ta ce ana sa ran kuma yin ruwa mai karfi da matsakaicin karfi a yankun Asir da Al-Baha da Jazan da Makkah da Najran da Madinah a ranar Lahadi da Litinin da Laraba da kuma Alhamis.

Haka kuma ta ce ana sa ran samun matsakaicin ruwan sama a yankunan Tabuk da Al-Jouf da kuma garuruwan da ke iyakar kasar ta arewa a ranar Litinin zuwa Laraba.

Ta kuma ce ana sa ran samun ruwan sama kadan amma mai dauke da guguwa a gabashin kasar daga Litinin zuwa Alhamis sai kuma a yankunan Makkah da Tabuk da Madinah a ranar Lahadi da Litinin da kuma Laraba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here