Abu uku masu karya azumi da mutum ba shi da iko a kansu

0
123

Ibadu da dama kan samu tangarɗa, saboda wasu kura-kurai ko ayyuka na mai gabatar da ibadar, kuma daga nan suna iya ɓaci.

Idan mutum yana sallah a ƙa’idar addinin Musulunci, zai iya aikata abubuwan da za su iya ɓata masa ibada, ta zama baɗilatun wato ɓatacciya.

Idan mai karatun Ƙur’ani ya sanya riya cikin karatunsa, hakan a cewar malamai zai iya ɓata masa karatu, a ƙarshe ya rasa ladan da ake kwaɗayin samu.

Azumi ma yana da wannan ɓangare, wanda mutum zai iya ɓata ibadarsa a cikin sani, ko kuma ba lallai da sani ba.

Gushewar hankali

Abu na farko, in ji Mallam Tukur Al-mannar shi ne, gushewar hankali ga mai azumi.

Idan mutum ya rasa hankali da azumi a bakinsa, hakan na iya kaiwa ga lalacewar ibadarsa.

Wasu Malaman sun tafi a kan cewa “wanda hankalinsa ya gushe daga lokacin sahur zuwa faɗuwar rana ne azuminsa ya lalace.

“Amma idan ya ɗauki azumi, sai matsalar gushewar hankali ta same shi, kuma ya farfaɗo wato ya samu lafiya ya dawo cikin nutsuwa da hankalinsa, gabanin a sha ruwa to azuminsa yana nan a wajen wasu malaman,” in ji Al-mannar.

Wasu daga cikin waɗanda za su iya samun kansu cikin irin wannan matsala ta gushewar hankali bagatatan, sun haɗa da wanda hatsari ya ritsa da shi kuma ya samu buguwar da ta kai ga ya rasa hankalinsa.

Akwai kuma matan da ke fuskantar bugu ko shafar aljani, wanda ke kaiwa ga gushewar hankali, har sai an yi musu magani ko ruƙiyya, ko kuma wani dalili ya sa aljanun sun fita.

Haka zalika, ana iya samun mutanen da za su wani abu mai tsayi ciki har da gini ko bishiya ko dutse, amma a samu akasi su faɗo, kuma su samu matsalar gushewar tunani.

Waɗannan da wasu matsalolin da ka iya haddasa gushewar hankali, ɗan’adam bai fiye samun iko a kansu ba, ma’ana ba zai iya hana faruwarsu ba.

Amai

Amai, ɗaya ne daga cikin abubuwan da malamai suka yi saɓani a kai game da yadda zai iya ɓata azumi.

Wasu malaman sun ce “fitar amai daga baki kawai, ba ya karya azumi. Wasu kuma sun ce matuƙar mutum ne ya ƙaƙaro shi, to shi ne ke da alhakin wannan azumin.

“Amma idan amai ya fi ƙarfin mutum har ya kai sanya shi galabaita, to zai fi alheri ya sauke azumi.

“Wasu kuma sun ce idan ya kasance amai ya fito, amma ya koma cikin maƙogwaron mutum, to shi kenan azuminsa ya karye kuma sai ya rama,” in ji Malam Tukur Al-mannar.

Jinin biƙi ko al’ada

Wannan matsala ce da ta shafi mata kawai, domin kuwa su ne suke haihuwa kuma suke yin jinin al’ada.

Ga mace wadda jinin al’ada ke ɓata wa azumi zai iya yiwuwa ta san lissafinta ta kuma ɗauki matakin gyara kanta, da kuma shirin yadda za ta fara shirin ramuwa.

Ita ma mai jinin biƙi, wato jinin haihuwa kenan, za ta iya sanin lokacin da za ta iya haihuwa, ko da cikin azumi ne.

Duk da yake, bai zama dole ta haihu a lokacin da likitoci suka ƙayyade mata ba.

Duka waɗannan abubuwan suna ɓata wa mace ibadar azumi, da zarar sun faru.

Kuma babu zargi ga duk wadda ta samu kanta cikin wannan hali, in ji Malam Al-mannar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here