Jami’ar Maryam Abacha ta rantsar da dalibai 1,200 a zangon karatu na 2022/23

0
125

Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) dake Kano, ta yi nasarar rantsar da sabbin dalibai 1,200 da suka samu gurbin karatu a zangon karatu na shekarar 2022/2023.

An gudanar da bikin rantsarwar ne a karo na biyu a ranekun Laraba 5 ga Afrilu da Alhamis 6 ga Afrilu, 2023 a tagwayen dakin taro na Farfesa Adamu Abubakar Rasheed, inda baki da aka gayyata ciki har da iyaye suka halarci taron.

An fara taron rantsarwar ne na kwanaki biyu da daliban Makarantar Kwamfuta a rana ta farko, a yayin da Makarantun Kimiyyar Zamantakewa da Gudanarwa, Kimiyyar Lafiya da Kimiyyar Jinya aka rantsar da su a rana ta biyu.

A nasa jawabin, shugaban Jami’ar MAAUN Farfesa (Dr.) Mohammad Israr ya ce taron na nuni da cewa daliban da suka samu gurbin karatu a jami’ar an rantsar da su a hukumance kamar yadda hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) ta amince.

Ya taya daliban murnar samun damar shiga jami’ar sannan ya bukace su da su rungumi kyakkyawan tarbiyya tare da fuskantar karatunsu da gaske.

“Ku tuna cewa a yanzu ku jakadu ne na Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya dake Kano, kuma dole ne ku bayyana a matsayin jakadu a dukkanin mu’amalarku a a cikin makarantar,” in ji Farfesa Israr.

Shugaban ya ce Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya tana gudanar da kwasa-kwasai ne kawai da ke da kimar kasuwanci ga dalibai yana mai jaddada cewa tsarin koyarwa a jami’ar ya shafi harkokin kasuwa ne da kuma dogaro da kai.

Ya gargadi daliban da su bi ka’idojin Jami’ar da kuma zama masu hali na kwarai, tare da sanya tufafi na mutunci.

A nasa jawabin wanda ya kafa kuma shugaban majalisar gudanarwa na jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya ce nan ba da dadewa ba za a kafa makarantar kasuwanci ta MAAUN a birnin Paris domin tallafa wa dalibai a yayin da za su gudanar da bincike a karatun digirinsu na biyu da nufin mayar da takardar shaidarsu ta dace da kasashen duniya.

Ya ce ya kamata sabbin daliban su yi la’akari da cewa sun yi sa’ar samun shiga Jami’ar yana mai cewa satifiket dinsu ita ce ta fi karbuwa a Afirka ta Yamma kuma ita ce kawai takardar shaidar da ba a tantancewa a matsayin wani sharadi na samun guraben aikin yi a Amurka.

Farfesa Gwarzo ya ce daliban da suka samu gurbin karatu ya kamata su yi alfahari da kasancewarsu cikin dangin MAAUN domin za su ci gajiyar jarin da suka zuba a fannin ilimi.

Ya shaida wa daliban da aka rantsar cewa akalla dalibai 500 ne da suka kammala karatu a Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijer dake Maradi ke aiki a wurare daban-daban a kasar Amurka.

Ya jaddada cewa MAAUN za ta ci gaba da bayar da ilimi mai inganci domin samar da kwararrun daliban da za su bayar da gudunmawarsu wajen ci gaban nahiyar Afrika da ma duniya baki daya.

Tun da farko, daya daga cikin ‘yan majalisar gudanarwa ta MAAUN, Farfesa Gaji Fatima Dantata, ta gabatar da sakon fatan alheri ga daliban da suka samu gurbin karatu, inda ta bukace su da su kasance masu da’a a kodayaushe domin kiyaye sunan Jami’ar da kuma cimma burinsu.

A sakon sa na fatan alheri, mataimakin shugaba, MAAUN Maradi, Dakta Shu’aibu Tanko ya taya daliban da aka rantsar da su a cikin dubban wadanda suka nemi shiga babbar jami’a.

Ya kuma bukaci sabbin daliban da su dauki karatunsu da muhimmanci domin samun damar yin aiki a manyan mukamai da dama a fadin duniya bayan kammala karatunsu.

Mataimakin shugaban jami’ar bangaren gudanarwa, Dakta Habib Awais Abubakar wanda shi ne ya jagoranci gudanar da taron rantsarwa, shi ne kuma ya jagoranci rantsar da daliban.

Sauran ma’aikatan Gudanarwa da suka halarta a yayin bikin sun hada da; Mataimakin Shugaba bangaren rayuwar cikin jami’ar, Dakta Hamza Garba, Mataimakin Shugaba a bangaren sha’anin Kudi, (Dr.) Abdulrasaq Kayode, Daraktan Tsare-tsare da Tabbatar da inganci, Dakta Nura Yaro, Daraktan Cibiyar Binciken manyan Ilimi da kirkira ta Afirka, Farfesa Abubakar Sadiq Haruna.

Sauran sun hada da Daraktan hulda da hadin gwiwa, Dr. Bala Mohammed Tukur, shugaban ofishin huldar kasa da kasa, Injiniya Bashir Garba, Shugaban Makarantu, Shuwagabannin sashe, Jami’an tsaro da baki da aka gayyata da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here