Wayewar masu zaɓe a Najeriya ta hana gwamnoni 10 zuwa majalisar dattawa – Buhari

0
135

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce zaɓukan 2023 sun nuna yadda mulkin dimokuraɗiyya ke ci gaba da ginuwa da ƙara ƙarfi musamman ganin yadda masu zaɓe suka waye da kuma sanin shugabannin da za su zaɓa.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi bakuncin sabon Sarkin Dutse, Alhaji Muhammad Hamim Nuhu a fadarsa da ke Abuja.

Ya ce sakamakon zaɓen da ya nuna gwamnoni guda 10 sun kasa samun nasarar zuwa majalisar dattawa, wata manuniya ce cewa yanzu babu tabbas game da samun mulki, kuma yanzu masu zaɓe ne ke da wuƙa da nama.

“Hakan ya nuna cewa dimokuraɗiyyarmu na ƙara bunƙasa da kuma yadda masu zaɓe suka waye.

Abin da ya ba ni mamaki shi ne ɗan Najeriyar da aka raina, a yanzu shi ne ke da wuƙa da nama wajen zaɓar wanda ya dace,” in ji Buhari.

“An mayar da abin kamar al’ada ta yadda idan gwamna ya kammala mulki tsawon shekara takwas a jiharsa, daga nan sai ya tafi majalisar dattawa, ba tare da wata wahala ba.

Daga yanzu babu wanda zai sake raina mai zaɓe a Najeriya. Siyasa za ta zama abu mafi wahala nan gaba,” a cewar Buhari.

Da yake jawabi, sabon Sarkin Dutse, Alhaji Muhamamd Hamim, ya yaba wa Shugaba Buhari saboda taimaka wa jihar Jigawa wajen samun ci gaba a ɓangaren noman shinkafa da amincewa da gina layin dogo daga Kano zuwa Dutse baya ga dawo da zaman lafiya a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here