DSS ta kama gagga-gaggan masu aikata miyagun laifuka a fadin Najeriya

0
122

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya a Nijeriya DSS ta ce ta kama gagga-gaggan masu aikata miyagun laifuka a wurare daban-daban a wasu sassan kasar, tare da kwace muggan makamai.

A wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun daraktan yada labaranta a ranar Lahadi da daddare, DSS ta ce cikin wadanda ta kama din har da wani tsohon kanal din soja mai ritaya da kuma wani lauya.

Wannan kame na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin tsaro a kasar suke nanata cewa suna samun nasarori wajen dakile aikata miyagun laifuka, musamman satar mutane don kudin fansa da ta addabi al’ummar kasar.

Hukumar ta kara da cewa ta yi wadannan kame ne daga tsakanin ranar Laraba 22 zuwa Lahadi 26 ga watan Maris, a jihohin Kogi da Adamawa da Filato da kuma babban birnin tarayyar kasar, Abuja.

Gungu na farko da DSS din ta kama na wasu mutum shida ne a garin Gegu Beki da ke kan babban titin Lokoja zuwa Abuja, a ranar Lahadi 26 ga Maris, kuma ta samu nasarar yin hakan ne karkashin hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da ke Jihar Kogi.

Mutanen da aka kama su ne Kanal AU Suleiman mai ritaya da Barista MK Aminu da Kabir Abdullahi da Isah Umar da Kadir Echi da kuma Adama Abdulkarim, inda aka same su da makamai ciki har da bindiga biyu da jigidar harsasai hudu da kuma kudi naira 11,030.

A ranar Asabar 25 ga Maris kuma DSS ta kama wani “gawurtaccen mai satar mutane don karbar kudin fansa” Haruna Adamu mai shekara 20, a karamar hukumar Gombi da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Nijeriyar.

“A lokacin da aka kama shi an same shi da bindiga kirar AK-47 daya da jigidar harsasai hudu,” a cewar sanarwar DSS.

Sanarwar ta ci gaba da cewa a ranar Alhamis 23 ga Maris mun kama wani mai laifi da ake nema mai suna Aminu Ibrahim a kan babban titin Kubwa da ke cikin Abuja.

“An kama shi ne yayin da ya fito daga Jihar Nasarawa dauke da jigidar harsasai 432 da aka dura su a galan din man ja da nufin kai wa wani mai satar mutane a Jihar Neja. Sannan an kwace tsabar kudi har naira N21,400 a hannunsa.”

Sai kuma kamen da hukumar ta yi a ranar Laraba 22 ga Maris a kusa da Bukuru a Jihar Filato, inda ta kama wani mai kai wa ‘yan bindiga sakonni a Jihar Zamfara, Babangida Ibrahim.

Sanarwar ta ce “an kwace jigidar harsasai 468 da kudi naira 21,090 a hannunsa.”

DSS ta ce za ta gurfanar da dukkan masu laifin a gaban kotu kamar yadda doka ta tanada, tare da shan alwashin hada kai da sauran hukumomi don ci gaba da binciken al’amura irin wadannan a sassan kasar.

“Hukumar za ta ci gaba da hada kai da dukkan masu ruwa da tsaki don dakile miyagun laifuka a kasar. Muna kuma kira ga mutane da su dinga bai wa hukumomi bayanai na duk wani alamar laifi da suka gani,” in ji sanarwar DSS.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here