Guinea ta ƙwace tan 1.5 na hodar iblis

0
99

Hukumomi a Guinea sun ƙwace tan 1.5 na hodar iblis a wani jirgin ruwa mai ɗauke da tutar Saliyo.

A tawagar matuƙa jirgin akwai yan Saliyo huɗu, da yan Ghana uku da kuma wasu ‘yan Guinea uku suma, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya tawaito.

Gidan talabijin na Guinea ya ce an kama mutanen baki ɗaya.

Hukumomin sun ƙara samun wasu jakankuna 60 da kowacce ke ɗauke da hodar da takai nauyin kilogiram 25 kwatan kwacin tan 3.9, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here