Ghana za ta girke sojoji 1000 a kan iyaka da Burkina Faso

0
135

Mahukunta a Ghana sun umarci sojoji dubu da ‘yan sanda su koma aikin tsaron iyakokin ƙasar a Arewa maso Gabas.

An ɗauki matakin ne sakamakon kashe wani jami`in hukumar hana shige da fice da wasu ‘yan bindiga suka yi, tare da jikkata wasu ma`aikatan biyu.

Babu tabbaci a kan ko su wane ne suka buɗe wa motar jami`an tsaron wuta a ranar Talata lokacin da suke aikin sintiri.

Amma akwai fargabar yawaitar ayyukan masu iƙirarin jihadi a ƙasar Burkina Faso wadda ke makwabtaka da Ghana.

Yankin Bawku ya jima yana fuskantar rikicin ƙabilanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here