Ba kasafai siyasar ubangida ke ƙarewa cikin ɗasawa ba – Masana

0
114

Wasu masana siyasa a Najeriya, sun ce har yanzu siyasar ubangida na tasiri a kasar musamman idan aka yi la’akari da abubuwan da suka gudana a zabukan da aka yi kwanan nan.

Masanan sun ce, siyasar ubangida ta yi tasiri kwarai da gaske a zaben gwamnoni musamman a jihohin Kano da Sokoto inda wasu tsofaffin gwamnoni da suka bar karagar mulki shekaru takwas da suka gabata suka nuna cewa har yanzu suna jan zarensu a siyasar jihohin.

Dr Abubakar Kari, masanin siyasa a jami`ar Abuja, ya shaida wa BBC cewa, a wasu lokutan idan aka yi rashin sa`a irin wannan siyasar tana da tata illar.

Malamin ya ce: “Ba kasafai dangantaka irin ta dasawa ke dorewa tsakanin ubangida da yaran gidan nasu ba, kuma ko da ta dore watakila a yi zama irin na hadin-bauta.”

Masanin siyasar, ya ce: “ A gaskiya mutane da dama na ganin rashin alfanun siyasar ubangida, a saboda a lokuta da dama an yi ta samun matsaloli wadanda irin wannan siyasa suka haddasa, saboda su iyayen giji sukan shake wuyan yaran gidansu su tabbata cewa duk abin da za su yi a matsayinsu na masu rike da mukami sai sun yardar musu.”

Ya ce, ”A wasu lokutan ma akan samu rarrabuwar kai har ma da rabuwa, to idan kuma ba a samu matsalar ba, ba a kowanne lokaci ba ne akan sakar wa yaran gidan mara su yi abin da suke so.”

Iyayen gida irin na siyasa dai su ne gaggan `yan siyasa da suka kama kasa kana su baza rassa a yankin da suke, wadanda saboda karfin da suke da shi sukan dauki dan siyasa su yi uwa da makarbiya wajen cicciba shi zuwa kan wani mukami.

A zaben gwamnonin da aka yi a Najeriya, tsohon gwamnan jihar Kano, kuma dan takarar shugaban kasa na jam`iyyar NNPP, Injiniya Rabi`u Musa Kwankwaso, da takwaransa, tsohon gwamnan jihar Sokoto Sanata Aliyu Magatakarda Wamako, wadanda suka shafe shekara takwas da sauka daga karagar mulkin jihohinsu, sun nuna wa duniya su ba kyallen yadawa ba ne a fagen siyasa a daidai lokacin da ake cewa siyasar ubangida ta kare a Najeriya.

Mutanen biyu sun jagoranci jam`iyyunsu a matsayinsu na `yan hamayya a matakin jiha suka fafata da `yan takarar da gwamnoni masu barin-gado ke mara musu baya, kuma suka yi musu kaye.

A baya haka aka fara tafiya zanzan tsakanin Gwanan jihar Kano mai barin-gado, Abdullahi Umar Ganduje da Injiniya Rabi`u Kwankwaso, kamar yadda gwamnan jihar Sokoto mai barin-gado, Aminu Tambuwal da Sanata Wamako suka faro, amma ba su gama wa`adin farko ba suka yi baram-baram.

Wannan ne ya sa wasu ke yanke kauna suna cewa wannan sabuwar tafiyar ma kwana nawa ne za ta watse.

Ko da yake iyayen gidan, musamman ma Injiniya Kwankwaso ya ce ba siyasar jiha ce a gabansa ba, har ma ya yi alwashin cewa ba zai yi wa gwaman mai jiran-gado, Abba Kabir Yusuf wato Abba Gida-gida katsalandan a mulki ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here