Yadda zamba da kutsen intanet ke neman talauta bankunan Afirka

0
97

A ranar 12 ga watan Agustan 2022 masu kutse sun samu damar yin kutse a shafin intanet na babban bankin kasar Afirka ta Kudu, SARB.

A yayin da bayan watanni SARB ya yi ikirarin cewa kutsen bai yi tasiri a kan ayyuakansa ba, abu mafi jan hankali shi ne yadda bankin bai san lokacin da aka yi hakan ba har sai da hukumar bincike ta Amurka FBI, ta ankarar da shi.

Ba shakka bankin bai san me yake faruwa ba a lokacin da aka yi kutsen. Ba Afirka ta Kudu ce kawai kasar da aka taba yi wa kutse don gano wasu bayanan gwamnati ta intanet ba a nahiyar.

Watanni kadan kafin hakan, a watan mayun 2022, wata kungiya ta masu aikata laifuka musamman irin na kutsen intanet mai suna Hive ta yi wa babban bankin kasar Zambia irin wannan ta’adi.

Shafin intanet na Bloomberg mai bin diddigin al’amuran kasuwanci a duniya, ya ce kungiyar Hive ta tattara bayanai na sirri sosai daga shafin bankin, tare da lalata wasu mahajojinsa da suka hada da wadda take hada-hadar musayar kudade.

Haka kuma masu kutsen sun bukaci bankin ya ba su fansa, shi kuma ya ki yin hakan.

A watan Nuwamba, sau biyu ana yi wa Babban Bankin kasar Gambiya kutse.

A na farkon, zan yi zargin cewa masu kutsen sun nemi a ba su dala miliyan 2.5 na fansa idan ba haka ba za su saki bayanan bankin.

Daga nan kuma sai aka cire ma’aikatan gwamnati daga cikin asusun ajiyarsu.

A watan Agustan 2022 masu kutse sun samu damar yin kutse a shafin intanet na babban bankin kasar Afirka ta Kudu/Photo AA

Baya ga wadannan, akwai kuma bankunan ‘yan kasuwa a kasashe irin Angola da Moroko da aka samu rahotannin cewa an yi musu kutse inda aka yi musu barazanar sakin wasu bayanansu na sirri ga al’umma.

Sannan a misali duk shekara a Nijeriya bankunan ‘yan kasuwa na tafka asarar dala miliyan 30 a sakamakon laifukan intanet.

Mene ne musabbabin kutsen?

Har yanzu ba a san musabbabin wadannan kutse da ake kai wa bankunan Afirka ba.

Amma wasu cibiyoyi irin su Africa Intelligence da ke bincike kan al’amuran da ke faruwa a nahiyar, ta yi hasashen cewa ana samun karuwar wannan aika-aika ne saboda yakin Yukren da Rasha na 2022.

Ta ce yakin ya tilasta wa masu kutse da ke gabashin Turai da dama suka bar yankin don neman sabbin wajen da za su yi sharafinsu.

A watan Afrilun 2022, hukumar FBI ta yi ikirarin cewa Afirka ta Kudu da sauran kasashen Afirka na daga cikin wata kungiya mai kasa 135 wadda masu kutse daga Rasha ke hankoro.

Kutsen intanet da ke faruwa a Afirka ba bankuna kadai ya shafa ba.

A watan Maris din 2022 kamfanin Afirka ta Kudu da ke bayar da bayanai kan hada-hadar kudade TransUnion, ya tabbatar da cewa wata kungiya ta masu kutse a intanet da ke Brazil N4ughtysecTU, ta sace bayanai masu nauyin tetarabayit hudu.

Sannan ta kuma nemi a ba ta fansar dala miliyan 15. Kazalika masu kutsen sun sanar da cewa suna fakon sauran kamfanonin Afirka irin su Absa.

Watanni kadan bayan nan, a watan Yuni, wasu ‘yan ta’addan intanet na kungiyar RansomHouse, suka yi wa babban kamfanin nan mamallakin shagunan kayan masarufi na Shoprite, da ke da shaguna kusan 3,150 kuma mai abokan hulda wajen miliyan 30, kutse.

Masu kutsen sun sace bayanan abokan hulda mai nauyin gigabayit 600, da suka hada da bayanan gwamnati, suka kuma bukaci a ba su fansa.

Daga tsakanin shekarar 2018 zuwa 2022, wata kungiyar masu kutse mai cibiya a Faransa OPERA1ER, ta yi ta kai wa bankunan Afirka farmaki.

A wancan lokacin an ba da rahoton cewa kungiyar ta sace dala miliyan 11 daga kamfanonin Afirka, sannan an kiyasta barnar da ta yi da cewa ta kai ta dala miliyan 30.

A yanzu haka Afirka na yin asarar dala biliyan hudu duk shekara sakamakon kutsen intanet, lamarin da ke jawo nakasu na a kalla kashi 10 cikin 100 na ma’aunin tattalin arzikin nahiyar.

Adadin zai yi ta karuwa saboda yadda kutsen intanet din ke kara kamari a Afirka.

Daga tsakanin Janairu zuwa Yunin shekarar 2022, shugaban kamfanin tsaron intanet na Kaspersky ya ce kutsen intanet din da ya fi shahara ya karu matuka, inda Kenya da Nijeriya suka fi fama da matsalar da kashi 438% da kuma kashi 174% a wannan tsakanin.

A wata biyu na biyun shekarar daga tsakanin watan Afrilu zuwa Yuni, an samu matsalar kutsen intanet da kashi 8.7 cikin 100 a Afirka a 2022.

A yayin da kutsen intanet nau’in phishing ya zama gama-gari a fadin duniya da ma Afirka, sai kuma ga zambar tsarin kudin intanet na crypto ma yana samun gindin zama.

A shekarar 2021 kawai, ‘yan Kenya sun yi asarar dala miliyan 120 a laifukan crypto yayin da ‘yan Afirka ta Kudu suka yi asarar dala miliyan 99, kamar yadda rahoton cibiyar the Global State of Scams ya bayyana.

Afirka ta Kudu ta kasance kasar da ta fuskanci zambar tsarin crypto mafi girma har sau biyu: na farko, kungiyar Mirror Trading International (MTI) ta zambaci dubban mutane kusan dala miliyan 589.

Daga baya, kamfanin zuba jarincrypto na Africrypt ya damfari masu zuba jari kusan dala biliyan 3.6 na crypto.

A fadin duniya gaba daya kuwa, an yi asarar kusan dala biliyan 20 na crypto a shekarar 2022. Baya ga crypto, batun satar kudi ta waya ma na daga cikin laifukan intanet da ke ta’azzara a Afirka.

Afirka ce kan gaba a harkar kudi ta waya da ya kai tiriliyoyin daloli. Sai dai shi ma wannan fanni na fama da nasa kason na zambar intanet.

Alal misali a Nijeriya, kamfanin sadarwa na MTN y ace an zambace shi dala miliyan 53 a cikin wata biyu kacal da kaddamar da harkar kudi ta waya da ya yi a aksar a shekarar 2022.

Na baya-bayan nan kuma shi ne wanda kamfanin sadarwa na Kenya na Safaricom ya sanar da cewa ya fada hannun baragurbi inda aka damfare shi dala miliyan hudu ta harkar kudi ta waya.

Labari mai dadin cewa gwamnatocin Afirka suna kokarinsu wajen magance matsalar.

Zuwa yanzu, kasa 33 daga cikin 54 na nahiyar Afirka da suka hada da Nijeriya da Afirka ta Kudu da Masar sun samar da wasu dokoki na tsaron intanet.

Ba dokokin intanet kawai kasashen ke samarwa ba, suna kuma kirkiro wasu dokoki na kariya da ke tursasa wa kamfanoni dabbaka dokokin tsaron intanet don su dinga bin ka’idojin tsaron intanet.

Rundunar ‘yan sanda kasa da kasa Interpol ta ce a kalla kashi 90 cikin 100 na kasuwanci a Afirka ana yi ne ba tare da bin ka’idojin tsaron intanet ba.

Akwai kuma kungiyoyi irin su Ciberobs da TradePass da ke hada taruka irin su taron Cyberx Africa Summit a Kenya, da kuma Cyber Africa Forum a Côte d’Ivoire.

Dubban mutane ne daga fadin duniya ke halartar wadannan tarukan inda suke wayar da kan kamfanoni da sauran masu ruwa da tsaki kan muhimmancin tsaron intanet.

“Wayar da kai shi ne babban aikin da muke yi a yanzu. Mutane na bukatar sanin barazanar da ke tattare da tsaron intaneyt,” in ji Franck Kiw, shugaban kamfanin Ciberobs a wata hira da ya yi da TechCabal a bara.

“Tabbas kasashe irin su Moroko da Mauritius da Kenya da Togo da Afirka ta Kudu da ma Kwadebuwa na sanya batun tsaron intanet a jerin manyan abubuwan da suka fi baiwa muhimmanci.”

Akwai yiwuwar Afirka ta samu damar shawo kan barazanar kutsen intanet da take fuskanta, a yayin da ake ci gaba da samar da dokoki da shirya taruka na kwararru kan samar da tsaron intanet.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here