Kotu a Jigawa ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wasu mutane 3

0
171

Kotu a jihar Jigawa ta arewacin Najeriya ta zartas da hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wasu mutane 3 da aka samu da aikata muggan laifuka ciki har da kisan kai, garkuwa da mutane da kuma fashi da makami ta hanyar amfani da manyan bindigogi.

Kirikasamma tare da neman biyan fansar naira miliyan 150.

Haka zalika yayin zaman shari’ar mutanen 3 sun kuma amsa laifinsu na kisan wani magidanci Audu Saje a karamar hukumar ta Kaugama.

Yayin sumamen da jami’an tsaro suka kai gidan mutanen 3 sun sanar da samun bindigogi kirar AK-47 guda 3 da wata babbar bindiga kirar GPMG sai carbin harsasai guda 9 kana harsasai na daban 309 sai kuma tsabar kudi Naira miliyan 2 da dubu 70 baya ga mashin wanda aka yi ittifakin na mutumin da suka kashe ne Audu Saje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here