Yadda ‘yan bindiga suka sace wasu ‘yan matan jami’a a Zamfara

0
212

’Yan bindiga a wannan Lahadin sun sace dalibai mata biyu na Jami’ar Tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara.

Rahotonni sun ce ’yan fashin dauke da muggan makamai, sun sace dalibai mata guda biyu a dakunan kwanansu da ke wajen makarantar.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, ‘yan ta’addan sun kai farmaki kauyen Sabon Gida da ke cikin garin Bungudu inda suka kutsa cikin dakin kwanan daliban mata.

Ya bayyana cewa, ’yan ta’addan sun somma kulle wasu masu gadin dakunan kwanan daliban tare da kwace musu wayoyinsu kafin su yi awon gaba da daliban.

A wata sanarwa da rundunar ’yan sandan jihar ta fitar, ta ambato Kwamishinan ’Yan sandan jihar, CP Kolo Yusuf na tabbatar wa da dangin daliban da kuma hukumar makarantar cewa rundunar na kokari wajen kubutar da daliban.

Sanarwar ta ce “rundunar ’yan sandan ta samu labarin sace daliban a dakunan kwanansu da ke a wajen makarantar.

“Tun bayan samun labarin sace daliban ne, rundunar ’yan sandan ta tura jami’anta zuwa wajen da lamarin ya faru, to sai dai kafin zuwan jami’an tsaron ’yan fashin sun tsere da daliban,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Haka kuma sanarwar ta ce Kwamishinan ’Yan sandan ya tura karin jami’an tsaro domin kubutar da daliban, tare da kama ’yan fashin domin gurfanar da su a gaban shari’a.

Daga karshe kwamishinan ’yan sandan jihar ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaron hadin kai domin samun nasarar kubutar da daliban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here