WhatsApp zai bullo da tsarin yin catin ko ba data da Intanet

0
171

Kafar sada zumunta ta WhatsApp na shirin bullo da wani sabon tsari da zai bai wa masu amfani da shi damar tura sako ba tare da amfani da intanet ba.

WhatsApp wadda mallakin kamfanin Meta ne, ya ce manufar tsarin ita ce kawo karshen yadda kasashe irin Iran ke toshe intanet dom hana mutanen kasar hulda da sauran sassan duniya.

“Tsarin zai taimaka wa jama’a a fadin duniya su yi magana da juna ko da kuwa an toshe intanet a kasarsu.

“Sun danne hakkin dan Adam na neman agajin gaggawa,” kamar yadda kafar BBC ta ruwaito kamfanin na cewa.

WhatsApp ya bukaci masu fasaha a fadin duniya da su ba da hadin kai da ba wa jama’a damar tattaunawa da juna kyauta, wanda kamfanin ya ce zai dauki gabaran jan ragamar tsarin.

“Maganar da mutum zai yi da wani za ta zama sirri tsakaninsa da wanda suke maganar.

“Babu wanda zai bankada sirrin maganarsu, babu wanda zai shiga tsakanin kama daga kan WhatsApp ko Meta.”

WhatsApp na ci gaba da bullo da sabbin sauye-sauye don inganta hulda a tsakanin ma’abota amfani da manhajar.

A baya-bayan nan ya fito da tsarin kallon ‘status’ din mutum ta kan hotonsa.

Kazalika, ya bullo da yanayin mutum sama biyu za su iya yin kiran waya ta manhajar, a wani lokacin ma zai adana kiran don mutum ya sake saurara a lokacin da yake so.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here