Soja ya harbe uwa da jaririnta a kan cin hancin N200 a Neja

0
139

Rahotanni daga Jihar Neja na cewa wani soja ya harbe wani dan acaba da wata fasinja dauke da jaririnta a unguwar Babanna da ke Karamar Hukumar Borgu ta Jihar.

Lamarin ya faru ne da yammacin Litinin a lokacin da wadanda abin ya shafa ke dawowa gida daga kasuwar mako-mako ta Babanna.

Mazauna garin sun shaida wa Aminiya cewa, sojan ya harbi dan acaban ne saboda ya ki ba shi cin hancin Naira 200 da ya nema, harsashin kuma ya ratsa cikinsa ya samu matar tare da jaririnta.

Wani mazaunin garin, Sa’idu Babanna ya ce, “Daya daga cikin sojojin da aka tura garin Babanna domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a ya harbe mutum uku saboda cin hancin Naira 200. A lokacin da wadanda abin ya shafa ke shiga Babanna da safe, sojoji sun bukaci Naira 200 kuma a lokacin da suke dawowa daga Babanna zuwa Nigangi a Jamhuriyar Benin, sojojin sun sake neman karin Naira 200 daga gare su, wanda suka ce ba za su iya biya ba

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here