Kar kuyi ko dar da amanar da al’ummar Kaduna ta damka mana – Uba Sani

0
352

Zababben gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya ce ba ya wata tantama shi ne zai yi nasara a kotu matuƙar ‘yan adawa suka ƙalubalanci sakamakon da ya ba shi a zaɓen jihar.

Hukumar zaɓe Najeriya Inec ta ayyana Uba Sani a matsayin wanda ya lashe zaben Asabar da ta wuce, bayan ya yi galaba a kan Isa Ashiru na jam’iyyar PDP.

Zaɓen tsakanin ‘yan takarar biyu ya yi zafi sosai inda aka yi ta jan lokaci kafin sanar da sakamako.

A hirarsa da editanmu Aliyu Abdullahi Tanko, Sanata Uba Sani ya ce zai yi mulki tare da kowa.

Alhamdu lillah, abin da ka sani ne cewa da muka sami wannan mulki na ce Allah ne ka ba da mulki ga wanda ya so kuma a lokacin da yaso.”

Ya ce bayan da ya fito neman mukamin, ya yi wa al’ummar jihar alkawari.

“Mun yi alkawarin za mu rike amana, mu kuma yi adalci. Za mu kuma rike kowa a daidai ba tare da mun zalunci kowa ba.”

Ya bayyana farin cikinsa kan yadda zaben ya kasance.

“Alhamdu lillahi, jama’a sun fito sun zabe ni, sun bani hadin kai, inda na yi farin ciki matuka, na san cewa an nuna min kauna a wannan zabe da aka yi.”

Game da ko ya fuskanci fargaba yayin da ake dakon sakamakon zaben, zababben gwamnana na Kaduna ya ce na kusa da shi ne ma suka fi shi damuwa.

“Duk abin da kaga ya faru ga dan Adam, to Allah ne ya kaddari haka, domin na sha shiga zabe kuma akwai lokutan da na fadi, akwai kuma lokutan da nayi nasara.”

Ya kuma ce ya kuduri aniyar yi wa jama’a adalci, ciki har da wadanda ba su zabe shi ba.

“Da wandanda suka zabe mu, da wadanda ba su zabe mu ba, kai har ma wadanda ba sa siyasa kwatakwata, za mu tabbatar mun yi musu adalci mu rike amanar da aka ba mu.”

Kan batun da ‘yan adawa a jihar ta Kaduna ke cewa bai lashe zaben gwamna ba, inda suke ikirari cewa kwace musu zaben aka yi.

Ya ce “Ka san ita siyasa ta gaji haka. Lokacin da na fadi zabe a 2011 na mukamin sanata, magoya baya na sun bukaci in shigar da kara a kotu, sai na zaunar da su, na yi musu wa’azi ina cewa Allah ke bayar da mulki kuma idan lokaci yayi, zai ba ni nasara, kuma da Allah ya tashi yin abin shi, a 2019 sai gashi na zama sanatan.”

Ya kara da cewa sau biyu yana takara, kuma sau biyu bai sami nasara ba.

“Da wanda na sami nasara, da wanda ban samu ba, na kan mika wa Allah ne lamari na.”

Kan batun ko zai iya kwato kujerar mukamin gwamna idan aka je kotu, zababben gwamnan ya ce ko shakka babu yana da yakinin zai sami nasara.

“Ai wannan zabe an yi shi karara. Ni a zargin da nake yi, ina ganin babu yadda za a ce jam’iyyar adawa ta PDP ta iya samun kuri’u masu yawa kamar yadda ta samu.”

Ya bayar da mmisalai karamar hukumar Chukun, “Kuri’un da suka samu a Chukun, kuru’a ce da rubuta ta aka yi -kuri’a sama da 89,000 wanda babu yadda za a yi hankali ya dauki haka.”

Ya ce ratar da ya kamata ya ba dan takarar PDP ma zai nuka haka idan aka je kotu.

“Ni abin da nake son gaya maka shi ne zan riga su zuwa kotu domin in kalubalanci wasu kauri’un da suka yi aringizonsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here