Sojoji sun kashe hatsabinin dan ta’adda Umaru Nagona

0
116

Dakarun sojin Najeriya sun hallaka, Umaru Nagona, daya daga cikin jagororin ’yan ta’adda da ya addabi yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Na gona, wanda a lokacin rayuwarsa ya addabi kauyukan kananan hukumomin Isa da Sabon Birni, da ke Gabashin Jihar Sakkwato ya gamu da ajalinsa ne bayan sojoji sun ritsa shi da yaransa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here