Jami’an tsaro sun rufe hanyar zuwa hedikwatar INEC a Kano

0
103

Jami’an tsaro sun datse hanyar zuwa shalkwatar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ke Kano da motocin sulke, da wayoyin tsaro na karfe.

Wakilinmu ya rawaito cewa mazauna unguwar da ke kusa da hanyar na cikin damuwa, saboda zaman gidan tilas da ya same su.

Kazalika wakilin na mu ya ce jami’an tsaron DSS sun hana ’yan jarida shiga ofishin INEC din, inda suka ce umarni ne da aka ba su daga sama, sai dai zuwa karfe 1:30 na rana za su bude.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here