‘Yan sanda sun cafke wadanda ake zargi da kai wa ayarin El-Rufa’i hari

0
93

Rundunar ‘yansandan Jihar Kaduna, ta bayyana cewa ta kama wasu daga cikin ‘yan shi’a da ta ke zargi da kai wa ayarin motocin gwamnan jihar, Malam Nasir Ahmed El-rufai hari.

A cikin sanarwar da kakakin ‘yansandan Jihar, DSP Mohammed Jalige ya fitar ya ce, jami’an ‘yansanda na ayarin motocin gwamnan jihar, sun yi bincike a Bakin Ruwa da ke Rigasa daura da babbar hanyar Nnamdi Azikiwe bayan da wadanda ake zargi da kai harin dauke da makamai ‘yan kungiyar shi’a ne sun kai wa wasu mazauna jihar masu bin doka da oda hari, tare da hana ababen hawa wucewa.

Ya ci gaba da cewa, ‘ya’yan kungiyar su da yawa, a jiya Alhamis sun tare hanyar suna cin zarafin jama’a da misalin karfe 3 na rana, daidai lokacin da ayarin motocin gwamnan jihar ya zo wuce wa.

Ya sanar da cewa, suna ganin ayarin motocin gwamnan sai suka fara jifan motocin gwamnan da duwatsu da kuma yin amfani da wasu makamai, inda suka lalata ababen hawa na jama’a da dama, inda jami’an tsaron na ayarin motocin gwamnan gwamnan suka mayar masu da martani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here