Kano: Gawuna ya cinye zabe a akwatunsa

0
87

Ɗan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar APC, Nasir Yusuf Gawuna ya yi nasarar cinye zaɓe a akwatun da ya kaɗa ƙuri’a.

Gawuna dai ya yi zaɓe ne a akwatu mai lamba 041 dake mazaɓar Gawuna a ƙaramar hukumar Nassarawa.

Sakamakon da aka wallafa a shafin intanet na INEC ya nuna Gawuna na da ƙuri’u 98 yayinda ɗan takarar NNPP Abba Kabir Yusuf ya samu ƙuri’u biyu.

Shi kuma ɗan takarar PDP, Sadik Aminu Wali ya samu ƙuri’u ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here